Sharrin Boka: Gwamna Ya Fadi Yadda Ya Tsira bayan Samun Jemage kan Gadonsa

Sharrin Boka: Gwamna Ya Fadi Yadda Ya Tsira bayan Samun Jemage kan Gadonsa

  • Sabon gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana yadda ya yi gwagwarmaya yayin yakin neman zabe bana
  • Gwamna Monday Okpebholo ya shaida yadda ya samu jemagen da ya mutu a kan gadonsa yayin da siyasa ta dauki zafi a Edo
  • Monday Okpebholo ya bayyana abin da ya kubutar da shi daga sharrin jemagen da kuma samun nasara a zaben Edo da ya gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi wani jawabi yayin taron nuna godiya bayan samun nasara a zabe.

Monday Okpebholo ya ce ya yi gwagwarmaya sosai ta inda ya taba samun mataccen jemage a kan gadonsa.

Monday Okpebholo
Gwamna ya samu jemage a kan gado. Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Monday Okpebholo ya yi bayanin ne a ranar Laraba da ta gabata a filin wasan birnin Benin.

Kara karanta wannan

Shiga ofis ke da wuya, Gwamna ya rushe ma'aikata, ya rufe asusun kudin jihar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya samu jemage kan gado

Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana cewa wata rana ya samu jemage a kan gadonsa ana tsaka da tattara sakamakon zabe.

Monday Okpebholo ya ce dogaro da Allah ne kawai ya kubutar da shi a lokacin da ya shiga cikin dakin.

"Bayan an kammala zabe ranar Asabar, ina shiga dakina a ranar Lahadi kawai sai na ga mushen jemage a kan gado.
Ban yi amfani da wani makami ba, kawai taimakon Allah ne ya ƙubutar da ni daga sharrinsa.
Saboda haka, ina ba ku shawara ku rika dogara da Allah, zai isar muku a kan dukkan komai."

- Monday Okpebholo

Gwamnan Okpebholo ya kara da cewa tun fara yakin neman zabe bai yi tunanin zuwa wajen boka ba ko wani mai magani ba.

The Nation ta wallafa cewa ya mika godiya ga Allah bisa yadda ya kare shi daga dukkan sharri kuma ya ba shi nasara.

Kara karanta wannan

'Babu mai karya ni': Wike ya fusata kan rigimar PDP, ya soki gwamna kan matsalarta

Gwamna ya rushe ma'aikatu a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa kwana biyu da shiga ofis, Monday Okpebholo ya rushe wata ma'aikata da gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira.

Gwamna Monday Okpebholo ya kuma umarci rufe asusun jihar da ke dukan bankunan yan kasuwa har sai an kammala bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng