Gwamna Abba Ya Mika Muhimmiyar Bukata ga Likitoci Masu Yajin Aiki a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya buƙaci likitocin da suka tsunduma yajin aiki da su janye domin a ceci bayin Allah
- Abba Kabir Yusuf ya buƙace su da su duba rayuwar marasa lafiya sama da miliyan 20 da za su cutu saboda yajin aikinsu
- An kawo masa rahoton kwamitin bincike kan zargin da ake yi wa kwamshiniyar jin ƙai da walwalar jama'a na cin zarafin likita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan yajin aikin da ƙungiyar likitocin jihar ta shiga.
Gwamna Abba Yusuf ya buƙaci likitocin da su janye yajin aikin inda ya yi gargaɗin cewa matakin da suka ɗauka zai jefa rayuwar mutane sama da miliyan 20 cikin hatsari a Kano.
Gwamna Abba ya nuna takaicin yajin aiki
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kuma ba ƙungiyar NMA tabbacin cewa an kawo masa rahoton kwamitin bincike kan zargin cin zarafin wata likita da ake yi wa kwamishiniyar jin ƙai ta jihar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Ƙungiyar likitocin dai ta ba da wa'adin sa'o'i 48 ga gwamnatin jihar kan ta kori kwamishiniyar ko kuma ta tsunduma yajin aiki idan ba a yi hakan ba.
Abba Kabir Yusuf ya nuna takaicinsa bisa shiga yajin aikin kan abin da ya kira rigima tsakanin mutane biyu da suka mallaki hankalin kansu.
Me Gwamna Abba ya gayawa likitocin?
"Na san lokuta da dama da aka fasa yajin aikin ƙungiyar NMA saboda kyakkyawar alaƙa mai kyau tsakanin likitoci da gwamnatin jihar Kano."
"Amma idan yanzu suna jin babu wanda zai iya yi musu magana kuma matakin da za su ɗauka shi ne yajin aiki, ya kamata su yi la'akari da rayukan mutane miliyan 20 waɗanda za su cutu saboda rashin jituwa tsakanin mutane biyu."
Da yake ba da haƙuri a madadin gwamnatin jihar, Gwamna Abba ya buƙaci likitocin da su duba illar da hakan zai yi wa marasa lafiya ciki har da masu juna biyu da ke jiran haihuwa, su janye yajin aikin.
Gwamna Abba ya magantu kan cin amanar Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana shirin ɓallewa daga gidan jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce taken da ake yaɗawa na, 'Abba tsaya da ƙafarka" babban cin mutunci ne a gare shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng