Shugaba Tinubu Ya Yi Ƙus Ƙus da Sanatocin PDP 3 a Abuja, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da sanatoci uku na jam'iyyar PDP a fadar gwamnatinsa da ke birnin tarayya Abuja
- Sanatocin sun shaidawa shugaban ƙasar ƴan bindiga sun hana manoma gudanar da ayyukansu a Kebbi ta Kudu da Kebbi ta Arewa
- Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya wallafa hotunan ganawar Tinubu da sanatocin adawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da sanatocin jam'iyyar PDP uku a Abuja ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2024.
Ƴan majalisar dattawan da suka ziyarci Tinubu a fadar shugaban ƙasa sun haɗa da Sanata Adamu Aliero, Sanata Yahaya Abdullahi da Sanata Garba Maidola.
Bola Tinubu ya gana da sanatocin PDP
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa hotunan wannan ziyara a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan wannan ganawa, sanatocin waɗanda suka fito daga jihar Kebbi a Arewa maso Yamma, sun lashi takobin dawo da zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
Haka nan kuma an ruwaito cewa sanatocin sun yabawa shugaba Tinubu bisa titin Sakkwato-Badagary da gwamnatinsa ta fara.
Abin da sanatocin suka tattauna da Tinubu
Dangane da batun tsaro, Sanata Aleiro ya ce:
"Za a iya magance matsalar tsaro a jihar Kebbi, a mazaɓar Kebbi ta Kudu, saboda kusancinmu da jihohin Neja da Zamfara, muna fuskantar kutsen ‘yan bindiga da ke kawo cikas ga noma.
"Haka ma a Kebbi ta Arewa da ke kusa da Sakkwato ta Gabas, ‘yan bindiga sun addabi manomanmu, shi ya sa muke ganin akwai bukatar a kara daukar matakai domin kawar da su daga wadannan yankuna.
"Shugaban kasa ya tabbatar mana da cewa za a kara daukar matakai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, ba a Kebbi kadai ba a duk fadin Najeriya."
Sanatocin na Kebbi sun kuma bayyana goyon bayansu ga gwamnatin Tinubu, inda suka ce duk da bambancin siyasa, za su ba da gudunmawa.
VAT: Sanata Ndume ya soki shirin gwamnatin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya ce ba zai zuba idanu ana kara bullo da manufofin da za su gallazawa talakawa ba
Ali Ndume ya nuna adawa karara da shirin gwamnatin Najeriya na kara kudin harajin VAT daga shekarar 2025 zuwa 2029.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng