An Shiga Jimami bayan Hadimin Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya yi wa ɗaya daga cikin jami'an gwamnatin jihar Legas rasuwa a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024
- Abdulrahman Lekki wanda shi ne shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Legas ya rasu da sanyin safiyar ranar Laraba
- Shugaban ma'aikatan jihar Legas wanda ya tabbatar da rasuwar a cikin wata sanarwa, ya ce marigayin ya rasu ne bayan jinya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Hadimin gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya riga mu gidan gaskiya bayan ya yi ƴar gajeruwar jinya.
Abdulrahman Lekki wanda shi ne shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Legas, ya rasu a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban ma’aikata na jihar Legas a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024 ta tabbatar da rasuwar marigayin, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya yi rashi a jihar Legas
Sanarwar ta bayyana cewa Abdulrahman Lekki ya yi bankwana da duniya ne bayan wata ƴar gajeruwar rashin lafiya.
Sanarwar na cewa:
"Tare da miƙa wuya ga ikon Allah, shugaban ma’aikatan jihar Legas na sanar da rasuwar Abdulrahman Lekki, shugaban hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Legas."
"Marigayin ya rasu ne a safiyar yau, 30 ga watan Oktoba, 2024, bayan gajeruwar rashin lafiya."
"Allah ya ji ƙan sa da rahama. Za a sanar da lokacin jana'iza daga baya."
MSSN ta yi wa gwamna ta'aziyya
Ƙungiyar ɗalibai musulmai reshen jihar Legas ta yi ta'aziyyar rasuwar marigayin a shafinta na X.
Ƙungiyar MSSN ta yi gwamnatin Legas da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, da hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Legas ta'aziyya kan wannan rashin da aka samu.
Ɗan tsohon gwamna ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi, mai suna Faisal Ahmed Mohammed Makarfi, ya rasu.
Wata majiya daga iyalansa da ta so a sakaya sunanta ta tabbatar da rasuwar inda ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon hatsarin mota.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng