Uba Sani Ya Fadi Sadaukarwar da Ya Yi bayan Zama Gwamna

Uba Sani Ya Fadi Sadaukarwar da Ya Yi bayan Zama Gwamna

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana matakan da ya ɗauka domin rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa
  • Uba Sani ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki yana karɓar rabin albashinsa ne kuma bai samu sabuwar mota ba
  • Ya bayyana cewa tsuke bakin aljihun gwamnatin ya taimaka wajen tura kuɗaɗe zuwa ɓangarori masu muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana matakan da ya ɗauka domin tsuke aljihun bakin gwamnati.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shi da ƴan majalisar zartaswarsa na kan tsarin karɓar rabin albashi da nufin rage kashe kuɗaɗen gwamnati.

Uba Sani ya tsuke bakin gwamnati
Uba Sani ya rage albashinsa Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Uba Sani ya tsuke aljihun gwamnati

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a bayan ya sanya labule da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamnan Kano ya yi rashi, babban ɗansa ya rasu a ƙasar Indiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matakin, a cewar gwamnan ya sanya an tura kuɗaɗe domin magance giɓin da ake da shi a fannin ababen more rayuwa, musamman a ɓangaren ilimi da kiwon lafiya.

Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana irin ci gaban da jihar ke samu a muhimman sassa daban-daban.

Uba Sani ya haƙura da sabuwar mota

Gwamnan ya ƙara da cewa tun hawansa mulki, babu wanda ya samu sababbin motoci daga shi har waɗanda ya naɗa muƙamai, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Ya bayyana cewa hakan ya ƙara taimakawa wajen rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.

"Mun yi alƙawarin rage kuɗin gudanar da harkokin mulki a jihar Kaduna. Ya zuwa yanzu, babu wani jami’in gwamnati, ciki har da ni da ya samu sabuwar mota. Wannan tsarin ya ba mu damar maida hankali kan inganta ilimi da kiwon lafiya."

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta taimaka wajen samo $57.5bn domin kafa Biafara? Gaskiya ta fito

- Gwamna Uba Sani

APC ta lashe zaɓen ciyamomi a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC ta lashe zaɓe a dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Jam'iyyar APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 255 a zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta gudanar ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng