Gwamna Ya Bi Sahu, Ya Bayyana Sabon Albashin da Zai Iya Biyan Ma'aikata

Gwamna Ya Bi Sahu, Ya Bayyana Sabon Albashin da Zai Iya Biyan Ma'aikata

  • Gwamna Umar Namadi ya sanar da N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin da zai biya ma'aikata a jihar Jigawa
  • Namadi ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati da ke Dutse bayan karban rahoton da kwamitin abashi da ya kafa
  • Gwamnan ya jaddada muhimmancin ma'aikata da kuma biyansu haƙƙinsu na ayyukan da suke yi duba da halin matsin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da ₦70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan gwamnati.

Gwamna Namadi ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar dake Dutse jim kadan bayan karbar rahoton kwamitin da ya kafa kan mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zama na farko a Arewa da ya amince da N80,000 a matsayin sabon Albashi

Gwamna Umar Namadi.
Gwamnan Jigawa ya amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: @uanamadi
Asali: Twitter

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Umar Namadi ya ƙara jaddada muhimmancin biyan ma'aikata haƙƙoƙin su na aikin da suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a biya ma'aikata N70,000 a Jigawa

“Bayan samun rahoton kwamitin da muka kafa, mun yanke shawarar biyan ma’aikatanmu ₦70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi,” in ji shi.

Malam Umar Namadi ya kuma bayyana kudirin gwamnati na kyautata jin dadi da walwalar ma’aikatanta.

Ɗanmodi ya ce sun yanke wannan shawarar na biyan N70,000 ne bayan yin la’akari da yanayin tattalin arziki da kuma karfin baitul-malin jihar Jigawa.

"Mun fahimci halin da ake ciki" - Namadi

Gwamnan ya kara da cewa:

"Mun fahimci tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasar nan kuma mun yi imanin cewa wannan karin zai taimaka matuka wajen rage wa ma'aikatanmu nauye-nauyen da wahalhalu."

Sanarwar ta samu karbuwa daga ma’aikatan jihar wadanda suka dade suna jiran labarin karin albashin.

Kara karanta wannan

Awanni da amincewa da mafi ƙarancin albashi, an shawarci gwamna ya dakata da biya

Namadi ya tabbatar wa al’ummar Jigawa cewa za a fara aiwatar da sabon tsarin albashin da wuri-wuri kuma za a yi duk mai yiwuwa don ganin kamai ya tafi daidai.

Jihar Neja za ta biya ma'aikata N80,000

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Umaru Bago na Neja ya amince da N80,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan jihar.

Bago ya sanar da haka ne bayan ganawa da shugabannin ƙungiyoyin kwadago reshen jihar Neja a fadar gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262