Rigima Ta Kauren Tsakanin Wasu Sarakuna kan Yankunan da Suke Mulki a Najeriya

Rigima Ta Kauren Tsakanin Wasu Sarakuna kan Yankunan da Suke Mulki a Najeriya

  • Rigima ta kaure tsakanin wasu sarakunan gargajiya a jihar Osun a game da kauyukan da ke karakashin masarautunsu
  • Rahotanni sun bayyana cewa an bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya kira zama na musamman domin a warware takaddamar
  • Tun farko dai Oba Ojelabi ya yi ikirarin kauyuka sama da 40 da ke yankin ƙaramar hukumar Ejigbo suna cikin masarautarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Rigima ta ɓarke tsakanin wasu sarakuna kan yankunan da ke karƙashin masarautun su a jihar Osun.

Wannan dalili ne ya sa aka nemi Gwamna Ademola Adeleki ya shiga tsakani don gudun lalacewar lamarin.

Gwamna Adeleke.
Rikici ya barke tsakanin sarakuna a Osun, an roki Gwamna Adeleke ya shiga tsakani Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

A rahoton Vanguard, Ogiyan na Ejigbo, Oba Omowonuola Oyeyode ya roki gwamnan ya kira zama da basaraken Songbe, Oba Kamil Ojelabi don warware matsalar.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun haɗa baki, sun kai karar basarake gaban gwamna, sun roki alfarma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake hira da ƴan jarida a fadarsa ranar Alhamis, Oba Oyeyode ya buƙaci gwamnatin Osun ta kira Oba Kamil ya kare kansa kan kalaman ya yi na mallakar wasu kauyuka.

Me ya haɗa sarakuna rigima a Osun?

Tun farko Oba Ojelabi ya yi ikirarin cewa kauyuka kusan 40 a yankin Ejigbo duk suna karkashin yankinsa, amma da yawan sarakunan yankin sun ce ƙarya yake.

A cewar Ogiyan, ya kamata a gayyaci Olusongbe na Songbe a yi masa tambayoyi kan wannan batu da ya kinkimo, sannan a sanar da al'umma duk abin da ya faɗa.

"Ina rokon gwamna da gwamnatin jihar Osun su gayyato hukumomin tarayya su zauna da shi, sannan ya yi bayani a bainar jama'a.
"Bai kamata mutum kamarsa ya fito yana ikirarin mallakar abin da ba na shi ba ne, kuma yana faɗawa jama'a bayanan ƙarya."

Kara karanta wannan

Jerin ministocin da Tinubu ya kora daga aiki da jihohin da suka fito a Najeriya

"Ina da hujja" - Oba Ojelabi ya maida martani

Da yake mayar da martani, Olusongbe ya ce yana da hakki akan kauyukan da ke yankin Songbe kuma ba zai bari wasu su gurbata tarihi ba saboda yana da hujjoji.

A ruwayar Punch, basaraken ya ce:

"Garuruwan da na ambata ana kiran su yankin Songbe, ba yankin Ejigbo ba. Na lissafa kauyukan da ke karƙashin masarauta ta kuma ina da hujja a kan haka.
"Idan su na da ta su hujjar su kawo mu gani, shi fa Ogiyan maƙaryaci ne, mutane da dama sun zo nan neman gonakin noma ne amma sai ya fara naɗa su a sarauta."

Sarkin ife ya faɗu wulaƙancin da aka masa

A wani labarin kuma mai Martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fadi wasu abubuwan da suka faru tsakanin shi da wani sarki.

Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wata rana ya ziyarci fadar Oluwo na Iwo Oba Abdulrasheed Akanbi amma abin bai yi kyau ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262