Ga Mari Ga Tsinka Jaka: Minista Ya Zagi Mazaunan Abuja da Za a Ruguzawa Gininsu

Ga Mari Ga Tsinka Jaka: Minista Ya Zagi Mazaunan Abuja da Za a Ruguzawa Gininsu

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya caccaki mazauna yankin Lugbe da ke birnin bisa zanga zangar adawa da rushe-rushensa
  • Hukumar gudanarwar Abuja ta fara rushe wasu wuraren da ta ce an yi gine-gine a filayen da ta ce an mallaka ba bisa ka'ida ba
  • An hango Ministan yana yi wa masu gudanar da zanga zangar fada, tare da bayyana masu hanyar da ake mallakar fili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kara jawo surutu bayan an hango shi a wani bidiyo ya na yi wasu mazauna birnin tsawa.

Minstan ya rika yi wa mazauna yankin Lugbe a Abuja bisa zarginsu da cinye filayen da ba mallakinsu ba ne a yankin.

Kara karanta wannan

Ana dakon korar Ministoci, Tinubu ya rushe ma'aikatu, ya yi garambawul a gwamnati

Nyesom
Nyesom Wike ya caccaki masu adawa da rusau a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike CON
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Nyesom Wike ya ziyarci Lugbe bayan ya samu labarin cewa wasu da ke da'awar mallakar filaye a wurin sun gudanar da zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna Abuja sun nemi a daina rusau

Mazauna Lugbe da ke babban birnin tarayya Abuja sun gudanar da zanga zanga, su ka bukaci mahukuntan babban birnin da kar su rushe masu gine-ginensu,

Mazauna wurin sun shaidawa Ministan Abuja, Nyesom Wike cewa su na da takardun da ke tabbatar da cewa sun mallakin filayen ta halastacciyar hanya.

Wike ya caccaki wasu mazauna Abuja

Nyesom Wike ya bukaci masu zanga zanga a Lugbe da ke Abuja da cewa ba su san sahihiyar hanyar da ake bi wajen mallakar filaye ba.

An gano shi a wani bidiyo da aka wallafa a shafin X, ya na bayani ga masu zanga zangar, ya rika yi wa masu ihu, ya na kiransu da 'marasa hankali.'

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Abuja: Wike ya bayar da wa'adin rusau

A baya mun ruwaito cewa hukumar gudanarwar Abuja ta ba masu gine-ginen da ba a kammala ba wa'adin watanni uku su gaggauta kammala su ko hukumomi su yi masu rusau.

Hukumar gudanarwar Abujan ta ce daukar matakin ya zama dole duba da yadda gine-ginen da ba a kammala su ba ke zama matattarar bata gari da ke zama barazana ga mazauna yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.