Obasanjo Ya Bayyana Babban Abin da Ke Barazana ga Tsaron Najeriya
- Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya koka kan yawaitar yaran da da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan
- Obasanjo ya bayyana cewa yaran da ba sa zuwa makaranta nan gaba za su iya zama haɗari ga tsaron ƙasar nan
- Ya bayyana cewa za a iya ɗaukar su domin shiga harkokin Boko Haram da ƴan bindiga nan da shekara 10 zuwa 15 masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan na da matuƙar haɗari ga al'ummar ƙasar nan gaba.
Obasanjo ya ce yara sama da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta nan gaba za su iya shiga harkokin Boko Haram da ƴan bindiga a cikin shekara 10 zuwa 15 masu zuwa.
Obasanjo ya ƙaddamar da ayyuka a Bauchi
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a Bauchi ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya je jihar Bauchi ne domin bikin ƙaddamar da wasu zaɓaɓɓun ayyuka da Gwamna Bala Mohammed ya gudanar.
Obasanjo ya nuna damuwa kan tsaron Najeriya
"Bankin duniya ya ce muna da yara sama da miliyan 20 waɗanda ya kamata su je makaranta amma ba sa zuwa makaranta a cikin al'umma mai yawan kusan mutane miliyan 230."
"Hakan na nufin cewa kaso 10% na yawan al'ummar da ya kamata su kasance a makaranta amma ba su zuwa."
"Gwamna, mai martaba, ƴan uwana wannan na nufin cewa nan gaba za su iya shiga cikin Boko Haram. Babu wanda yake buƙatar ya gaya mana hakan."
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya ƙara da cewa rashin ba yaran damar samun hanyoyin da za su gina kansu, ya sanya za su iya faɗawa tarkon yi wa Boko Haram da ƴan bindiga aiki cikin sauƙi.
Obasanjo ya kamu da cuta bai sani ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan cutar da ta taɓa kama shi ba tare da ya sani ba.
Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya taɓa samun matsalar rashin ji ta kaso 25% cikin 100% ba tare da saninsa ba.
Asali: Legit.ng