Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Ƴan Najeriya Albashir da ASUU Ke Shirin Rufe Jami'o'i
- Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka tana koƙarin dakile sabon yunkurin malaman jami'a na shiga yajin aiki
- Karamar ministar kwadago, Hon. Nkeiruka Onyejeocha ce ta bayyana hakan a wani taron kiwon lafiya da ta halarta a jihar Abia
- Ta ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar saita tattalin arziki ta hanyar tsare-tsaren da ya ɓullo da su a gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abia - Ƙaramar minsistar kwadago da samar ayyukan yi, Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta ce gwamnatin tarayya na koƙarin dakile yunƙurin ASUU na shiga yajin aiki.
Ta ce gwamnatin ba za ta bari kungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa watau ASUU ta shiga yajin aiki ba, za ta yi duk mai yiwuwa wajen biya mata buƙatunta.
Minista ta hango amfanin manufofin Tinubu
Onyejeocha ta kuma ƙara da cewa manufofin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu za su magance matsalolin tattalin arziki tun daga tushe, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarta, nan gaba ƴan Najeriya za su amfana da tsare-tsaren Tinubu duk a yanzu suna fuskankar matsi.
Ministar ta yi wannan jawabi ne a lokacin da take amsa tambayoyi daga manema labarai a wurin bikin kiwon lafiya karo na 17 a Isuochi, jihar Abia.
Wane mataki gwamnati ta ɗauka kan ASUU?
Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a warware dukkan batutuwan da ASUU take kuka a kansu, in ji Punch.
A makon jiya ne ASUU ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ta biya bashin da malaman jami'o'i suka biyo a lokacin yajin aiƙin 2020.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta cire mambobinta daga tsarin biyan albashi na IPPIS, sannan a maida su kan wanda suka gabatar watau UTAS.
Gwamnati ta kusa shawo kan ASUU
Da take jawabi, ƙaramar ministar kwadagon ta ce:
"Dangane da batun barazanar ASUU na shiga yajin aiki, mun zauna mun tattauna kuma ina da tabbacin nan ba da jimawa ba za a warware komai.
"Game da yajin aikin da ke kunno kai kuma mun zauna da ƴan kwadago, mun fahimci juna sannan mun gaya masu halin da ƙasar nan ke ciki."
Wani malamin jami'a ya shaidawa Legit Hausa cewa ya zama tilas a kyautata masu idan da gaske ana son gyara ɓangaren ilimi a Najeriya.
A cewarsa, albashin da ake biyansu a wata ba ya ɗaukar nauyin kaso 50% na ɗawainiyar da ke kansu a kowane wata.
"Har yanzun muna bin bashin albashin wasu watanni tun lokacin Buhari, wannan gwamnati ta zo kamar za ta biya amma shiru, to da wanne za mu ji?
"Nawa ake biyan irin mu kananan malamai, nawa ake biyan manya? Abin da ake bamu ba ya zuwa ko ina a wata, ya kamata gwamnati ta duba bukatun ASUU," in ji shi.
ASUU ta shiga yajin aiki a Gombe
A wani labarin kuma kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) a jami'ar jihar Gombe ta tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biya mata bukatu.
Shugaban ASUU na jami'ar jihar Gombe, Dakta Salihu Sulaiman Jauro ya bayyana abubuwan da gwamnati ta gaza yi musu.
Asali: Legit.ng