Babbar Kotu Ta Hana Hukumar EFCC Kama Tsohon Ministan Obasanjo

Babbar Kotu Ta Hana Hukumar EFCC Kama Tsohon Ministan Obasanjo

  • Babbar kotun tarayya ta umarci hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) da ta rabu da tsohon Ministan tsaro
  • Tsohon Ministan tsaro, Lawal Batagarawa ne ya shigar da kara gaban Mai Shari'a Yusuf Halilu kan cin zarafinsa da EFCC ke yi masa
  • Lamarin ya biyo bayan wata takaddama kan fili mallakin tsohon Ministan da ya ce ya samu daga hannun gwamnatin tarayya a 2021

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta umarci hukumar EFCC da ta dakatar da duk wani yunkuri na gayyatar tsohon Ministan tsaro, Lawal Batagarawa.

Kara karanta wannan

Shari'ar N1.6bn za ta zo karshe, EFCC da tsohon Akanta Janar za su daidaita

Tsohon Ministan ya zargi hukumar EFCC da cin zarafinsa a lokuta daban-daban kan sabani da aka samu bisa mallakin wani fili a Abuja.

Hukuma
Kotu ta hana EFCC kama tsohon Ministan tsaro, Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a hukuncin da ya yanke ranar Talata, Mai Shari'a Yusuf Halilu ya haramtawa EFCC tunkarar inda Lawal Batagarawa ya ke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan tsaro ya maka EFCC a kotu

Tun da fari, tsohon Ministan tsaro, Yusuf Batagarawa ne ya shigar da kara ya na neman a yi masa katanga da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Tsohon Ministan ya bayyana shaidun da ke nuna hukumar EFCC ta ci zafafinsa har da kiyaye-kirayen waya inda jami'an EFCC su ka yi masa barazana.

Da me ake tuhumar tsohon Minista?

Wani Patrick Ineke ne ya shigar da korafi ya na ikirarin cewa wani fili da yanzu ke mallakin Yusuf Batagarawa mallakinsa ne.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta karo kayan aiki domin ragargaje yan ta'adda a Arewa

Tsohon Ministan tsaron ya musanta batun, inda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta mallakawa kamfaninsa filin a shekarar 2021.

EFCC ga shiga yarjejeniya da tsohon Akanta

A baya mun wallafa cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) za ta shiga yarjejeniya da tsohon Akanta janar na kasa, Anamekwe Nwabuoku.

Hukumar EFCC ta shigar da kara gaban Mai Shari'a James Omotosho ana zargin tsohon Akanta janar, Anamekwe da wani Felix Nweke da wawashe Naira Biliyan 1.6 daga asusun gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.