An Yi Rashi: Dan Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Rasu a Hatsarin Mota

An Yi Rashi: Dan Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Rasu a Hatsarin Mota

  • Allah ya yi wa ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi rasuwa sakamakon wani hatsarin mota
  • Marigayi Faisal Ahmed Mohammed Makarfi ya rasu ne a ranar Asabar, 12 ga watan Oktoban 2024 a kan titin hanyar Kaduna zuwa Zaria
  • Rasuwar Faisal ita ce mutuwa ta biyu da ta faɗa kan iyalan wani babban a Najeriya bayan ɗiyar Mele Kyari ta rasu a ranar Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi, mai suna Faisal Ahmed Mohammed Makarfi, ya rasu.

Wata majiya daga iyalansa da ta so a sakaya sunanta ta tabbatar da rasuwar inda ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon hatsarin mota.

Kara karanta wannan

An shiga rudani da yan bindiga suka hallaka dan takarar APC, ana daf da zaɓe

Dan Ahmed Makarfi ya rasu
Dan tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi ya rasu Hoto: Faisal Mohammed Makarfi
Asali: Facebook

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna ya rasu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hatsarin ya auku ne a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria a yammacin ranar Asabar, 12 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hatsarin ya auku ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria da yammacin yau. An kai shi wani asibiti inda a nan aka ce ya rasu."
"Mahaifinsa yana asibitin, an kai gawarsa gida domin yi masa jana'iza."

- Wata majiya

Ba a samu jin ta bakin Ahmed Mohammed Makarfi ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.

Wane ne Faisal Ahmed Mohammed Makarfi?

Marigayi Faisal wanda Injiniya ne ya halarci makarantar Kaduna International School sannan ya wuce Kwalejin Adesoye da ke Offa a jihar Kwara domin yin karatunsa na sakandare.

Ya halarci jami'ar Greenwich da ke Landan, inda ya yi karatun digirinsa na farko, digirin digirgir sannan ya yi rajistar yin digirin digir a jami'ar.

Kara karanta wannan

Shugaban kamfanin NNPCL, Kyari ya yi babban rashi, Kashim Shettima ya jajanta

Wannan dai shi ne lamari na biyu mai ban tausayi da ya auku kan iyalan wani babba a Najeriya a ƙarshen makon nan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), ya rasa ƴarsa Fatima mai shekara 23 da haihuwa.

Tinubu ya yi ta'aziyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahamed Tinubu, ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar Hajiya Salamatu Asabe, ƙanwar tsohon shugaban kasa na soji, Janar Abdulsalami Abubakar (Mai ritaya).

Shugaba Bola Tinubu ya kuma yi ta'aziyya ga sauran dangin mamaciyar baya ga Abdulsalami bisa wannan rashi babba da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng