Gwamna Ya Rugurguza Katafaren Ginin Babba a APC cikin Dare, An Fara Cacar Baki
- Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da ruguza wani babban ginin tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Moshood Mustapha
- Hon. Moshood ya ce akwai wasu dalilai na siyasa da suka jawo gwamnatin jihar rusa masa ginin wanda ke dauke da shaguna
- Haka zalika tsohon gwamnan jihar Kwara, Abubakar Bukola Saraki ya yi martani kan ruguza ginin inda ya ce hakan bai dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdularzaq ya yi rusau kan ginin wani babba a jam'iyyar APC.
Hukumar lura da tsare-tsaren birni ta KW-GIS a jihar ta ba da hanzarin cewa tun asali ma an yi ginin ne ba a kan ka'ida ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wanda suke haya a ginin sun ce an ba su wa'adin sa'o'i uku ne kawai su tattare kayansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rusa ginin babban a jam'iyyar APC
Gwamnatin Kwara ta ruguza babban ginin Crystal Palace na wani kusa a jam'iyyar APC a daren ranar Lahadi.
Hukumar KW-GIS ta ce ginin ya saba doka kuma dama an ba jigon na APC wajen ne domin ya yi filin ajiye motoci ba shaguna ba.
Jigon APC ya yi maratani kan rusa gininsa
Hon. Mashood Mustapha ya ce babu zancen cewa ginin ya saba doka, ya ce tun asali a mallaka masa filin ne domin yin kasuwanci.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin ta rusa masa shagunan ne saboda sabani na siyasa tsakaninsa ga gwamnan jihar.
Dama dai akwai sabani da aka samu tsakanin Mashood Mustapha da gwamnan jihar kan wata kwangilar N17.8bn.
Saraki ya yi magana kan rusa gini a Kwara
Leadership ta wallafa cewa tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki ya ce abin mamaki ne ace su na jam'iyya daya kuma gwamnan ya rusa masa gini.
Saraki ya yi zargin cewa akwai alaƙar siyasa a lamarin musamman ganin yadda masu zaben suka juyawa APC baya a zaben kananan hukumomin jihar.
An dakatar da kusa a APC a Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa APC ta dakatar da tsohon sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a jihar Kwara, Tajuedeen Aro bisa zargin cin amana.
An ruwaito cewa shugabannin APC na gundumar Ojumo ta Arewa maso Yamma ne suka sanar da haka a wata wasika da suka tura masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng