Cuta Ta Ɓarke a Jihar Borno bayan Ambaliyar Ruwan da Ta Afku, Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin Borno ta bayyana cewa an samu ɓullar cutar kwalara a wasu ƙananan hukumomi sakamakon ambaliyar ruwa
- Kwamishinan lafiya, Farfesa Baba Gana ya ce gwamnati ta fara kokarin yaƙar cutar tun da wuri domin daƙile yaɗuwarta
- Ya ce ana zargin cutar ta ɓarke ne sanadin ambaliyar ruwan da aka yi a makonnin da suka gabata a wasu sassan jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da ɓullar cutar kwalara watau amai da gudawa sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku kwanakin baya.
Kwamishinan lafiya na Borno, Farfesa Baba Gana shi ne ya bayyana hakan a asibitin ido da ke Maiduguri ranar Alhamis.
Ya ce ma'aikatar ta tura samfurin mutum 200 domin gwaji kuma sakamakon ya nuna mutane 17 daga cikin sun kamu da cutar kwalara, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene ya jawo ɓarkewar kwalara a Borno?
A cewarsa, ɓarkewar cutar a wannan karon yana da nasaba da ibtila'in ambaliyar ruwan da ta afku a Maiduguri da wasu sassan kananan hukumomin jihar
Farfesa Baba Gana ya bayyana cewa a halin yanzu an gano cutar ta ɓulla a ƙananan hukumomin Jere, Mafa, Konduga, Dikwa da MMC
Ya ce duk da babu wanda cutar ta kashe kawo yanzu, amma ana samun ƙaruwar kamuwa da ita a kananan hukumomi da dama.
Baba Gana ya ƙara da cewa zuwa yanzu su na da rahoton waɗanɗa ake zargin sun kamu da cutar har mutum 451 amma mutum 17 ne kaɗai aka tabbatar.
Wane mataki gwamnatin Borno ta ɗauka?
Wannan ya sa gwamnatin Borno karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umaru Zulum ta sanar da fara ɗaukar mataki cikin gaggawa don daƙile yaɗuwar cutar.
A cewar gwamnatin, ta tanadi allurar rigafin cutar guda 400,000 waɗanda za a yi amfani da su domin kare sauran al'umma.
Haka nan kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu kamar WHO da MSF sun fara tanadar wurare da kayan aiki domin killace waɗanda suka kamu da cutar.
Gwamna Zulum ya ziyarci wuraren ambaliya
A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci wasu wuraren da ambaliya ta yi gagarumar barna a jihar Borno.
Mai girma gwamnan ya yi takaicin yadda wasu mutane su ka gina gidaje a gabar ruwa, wanda hakan ya hana ruwa bin hanyarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng