Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Sanatan Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Sanatan Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa tsohon sanatan Adamawa ta kudu, Jonathan Silas Zwingina rasuwa yana da shekara 70 a duniya
  • Marigayin ya kasance darakta janar na kwamitin yakin neman zaben marigayi MKO Abiola a lokacin zaɓen 1993
  • Sanata Jonathan Silas Zwingina babban 'dan siyasa ne kuma yana cikin waɗanda suka kafa PDP a shekarar 1998
  • Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya a birnin tarayya Abuja ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Jonathan Silas Zwingina ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Marigayi Sanata Zwingina ya rasu ne yana shekaru 70 a duniya.

Taswirar Adamawa.
Tsohon sanatan Adamawa ta Kudu, Jonathan Silas Zwingina ya rasu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zwingina: Sarkin yakin zaben Abiola ya rasu

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

Zwingina ya kasance Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta ‘Hope 93’ na marigayi Cif Moshood Abiola a inuwar jam’iyyar SDP a zaɓen 1993.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ne ya soke zaɓen 1993 bayan Abiola ya samu nasara, rahoton Leadership.

Tsohon sanatan ya rasu ne a ranar Laraba da ta gabata, 2 ga watan Oktoba, yana da shekaru 70 a birnin Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Taƙaitaccen bayani kan marigayi Zwingina

Zwingina, tsohon Sanata mai wakiltar mazaɓar Adamawa ta kudu, yana daya daga cikin manyan ƙusoshin da suka kafa jam'iyyar PDP a 1998.

Ya zama sanatan Adamawa ta kudu a zaɓen 1999 kuma al'ummar mazaɓar sun sake zaɓensa a karo na biyu a shekarar 2003.

Ya yi aiki a kwamitocin Majalisar dattawa da suka haɗa da ayyuka da gidaje, harkokin cikin gida, watsa labarai, yyuka na musamman, kasuwanci da harkokin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da hutu a ranakun Alhamis da Juma'a a jiharsa, bayanai sun fito

An tattaro cewa a 2007 aka rushe gidan Marigayi Zwingina da ke Abuja a bisa umarnin tsohon ministan babban birnin tarayya, Malam Nasir El-Rufai.

Wadanda ke tare da shi a lokacin kafa PDP sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, marigayi Wilberforce Bafte Juta, Cif Joel Madaki, Marigayi Solomon Lar da dai sauransu.

Majalisa ta girmama Sanata Ubah

A wani rahoton kuma majalisar wakilai ta ɗage zamanta na farko bayan dawowa daga hutun shekara-shekara domin jimami da karrama marigayi Sanata Ifeanyi Ubah

Sanatan mai wakiltar Anambra ta Kudu a majalisar dattawa ya riga mu gidan gaskiya ne a watan Yuli lokacin ƴan majalisa sun tafi hutu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262