1 ga Oktoba: Gwamna Ya Ba Matasa Shawara kan Shirya Zanga Zanga
- Gwamnatin Adamawa ta yi kira ga mutanen jihar da ka da su shiga zanga-zangar da aka shirya gudanarwana ranar 1 ga watan Oktoban 2024
- Babban mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan zaman lafiya da tsaro ya buƙaci iyaye da ka da su bari ƴaƴansu su shiga zanga-zangar
- Ahmed Lawan ya bayyana cewa jihar ba ta taɓa amfana daga zanga-zangar da aka taɓa yi a baya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Gwamnatin Adamawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri, ta yi kira ga al'ummar jihar da ka da su shiga zanga-zangar da aka shirya ranar, 1 ga watan Oktoban 2024.
Gwamnatin ta buƙaci al'ummar jihar musamman matasa da ka da su shiga zanga-zangar wacce aka shirya gudanarwa.
Babban mai ba gwamna Ahmadu Fintiri shawara na musamman kan zaman lafiya da tsaro, Ahmed Lawan ya yi wannan kiran, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamnati ba ta son a yi zanga-zanga?
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa Adamawa ta samu zaman lafiya kuma ganganci ne duk wani mai kishin ƙasa ya yi tunanin cewa zai fito zanga-zanga, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
Ahmed Lawan, wanda ya ce jihar Adamawa ba za ta shiga zanga-zangar ba, ya ƙara da cewa jihar ba ta taɓa samun wani amfani ba daga zanga-zangar da aka taɓa yi a baya.
Ya bayyana cewa bai kamata a kawo naƙasu ga manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke yi saboda zanga-zangar ba.
"Muna kira ga iyaye, ƙungiyiyon addini da su ba ƴaƴansu da mabiyansu shawara ka da su fito zanga-zangar wacce wasu da ba a san ko su wanene ba suka shirya."
"Ya kamata duk wani mai kishin ƙasa nagari yayi watsi da shirin masu zanga-zangar waɗanda ba a san ko su wanene ba."
- Ahmed Lawan
Ƴan sanda sun yi gargaɗi kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gargadi masu shirin gudanar da zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.
Rundunar ta ja kunnen masu shirin fita kan tituna da cewa ba za ta lamunci karya doka da oda da sunan zanga-zangar tsadar rayuwa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng