1 Oktoba: Bayan Lissafo Matsaloli, Gwamna Ya Fadi Abin da Ake Bukata daga Yan Najeriya

1 Oktoba: Bayan Lissafo Matsaloli, Gwamna Ya Fadi Abin da Ake Bukata daga Yan Najeriya

  • Gwamna Mai Mala Buni ya shawarci al'umar jiharsa na Yobe da sauran yan kasar nan kan taimakon gwamnati
  • Gwamnan ya ce dole a taya shugabanni da addu'a idan ana fatan samun jagoranci na gari da wanzuwar zaman lafiya
  • Ya bayyana haka ne ta cikin sakon taya yan kasar nan murnar cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya nemi hadin kan yan kasar nan domin samar da jagoranci cikin nasara.

Ya bayyana haka ne yayin bikin zagayowar ranar samun yancin kan kasar nan, wacce ta kai shekara 64 da samu daga turawan mulkin mallaka.

Kara karanta wannan

Kungiyoyi a Kaduna sun barranta da zanga zangar 1 ga watan Oktoba

Mai Mala
Gwamnan Yobe ya nemi hadin kan yan kasa Hoto: Mamman Mohammed
Asali: Facebook

A sakon da daraktan yada labaran gwamnan, Mamman Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya ce sai an hada kai za a kai ga ci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya lissafo matsalolin Najeriya

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ce akwai tarin matsalolin da su ka addabi kasar nan daga tsaro zuwa tattalin arziki da zamantakewa.

Daga cikin matsalolin da ya ce ana fama da su akwai rashin tsaro, rushewar tattalin arziki sannan ya bayar da tabbacin talakawan kasar nan na cikin mawuyacin hali.

Gwamna ya gano yadda za samu sauki

Gwamna Mai Mala Buni ya ce hadin kan yan kasa da addu'a ga shugabanni zai taimaka masu wajen sauke nauyin al'uma.

A jawabinsa na cikar Najeriya shekara 64, ya ce shugabanni na bukatar hadin kan jama'a, musamman a wannan lokaci da ake fama da tarin kalubale wajen jagorancin kasar.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Ana murnar samun ƴanci, gwamna ya ƴanta fursunoni a Najeriya

Kungiyar NAS ta gano matsalolin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Association of Seadogs, Pyrates Confraternity ta shaidawa gwamnatin tarayya cewa akwai tarin matsaloli da su ka addabi yan kasar nan.

Kungiyar ta shawarci gwamnatin tarayya ta magance yunwa, fatara da rashin tsaro, sannan a dai na kama masu zanga zanga da ke nuna rashin jin dadinsu da tsarin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.