Matatar Mai: Tsohon Kakakin Jonathan Ya Ba Aliko Dangote Shawara

Matatar Mai: Tsohon Kakakin Jonathan Ya Ba Aliko Dangote Shawara

  • Tsohon kakakin tsohon ƙasa Goodluck Jonathan, ya ba Aliko Dangote shawara kan matatar man da ya gina a jihar Legas
  • Ima Niboro ya buƙaci hamshaƙin ɗan kasuwan na nahiyar Afirika da ka da ya fifita samun riba daga matatar man da ya mallaka
  • Ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da zai rama biki wajen kyautatawa ƴan Najeriya saboda ƙasar nan ta yi masa dukkanin wani gata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon kakakin Goodluck Jonathan, Ima Niboro, ya ba Aliko Dangote shawara kan matatar man da ya mallaka.

Ima Niboro ya buƙaci Dangote da ka da ya mayar da hankali wajen samun riba daga matatar man wacce ke a jihar Legas.

Kara karanta wannan

"Na fi ƙarfinku," Ministan Tinubu ya ƙara ta da Hazo, ya yiwa wasu gwamnoni shaguɓe

An ba Dangote shawara kan matatar mai
Tsohon kakakin Goodluck Jonathan ya ba Dangote shawara kan matatar mai Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Tsohon kakakin na tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba Dangote?

Ima Niboro ya bayyana cewa Najeriya ta yiwa Dangote gata, saboda haka a halin yanzu ya kamata ya mayar da biki.

"Ina so na yi kira ga babban ɗan uwanmu, Dangote, cewa a halin yanzu magana ce ta kasuwanci, amma ka da ya maida hankali wajen fifita samun riba mai yawa. Najeriya ta yi masa komai."
"Ya kamata a wannan lokacin ya nuna halin kyautatawa ga ƴan Najeriya. Idan ya yi asarar wasu ƴan biliyoyin Naira wajen yin hakan, zai samu ninƙinsu daga dizal, taki da sauran kayayyaki sama da 500 da matatarsa za ta samar da zai sayar ga ƴan Najeriya da sauran duniya."
"Ƴar sadaukarwar da zai yi a wannan lamarin ba za ta sanya ya talauce ba. Ka da ya fifita riba a wannan lokacin."

Kara karanta wannan

Wani ƙasurgumin ɗan ta'adda ya ajiye makamai, ya miƙa wuya ga rundunar sojoji a Arewa

- Ima Niboro

Karanta wasu labaran kan Dangote

Fasto ya ba gwamnati shawara kan Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban limamin cocin Katolika na Ibadan Archdiocese, Rabaran Gabriel Abegunrin, ya ba gwamnatin tarayya shawara kan matatar Dangote.

Malamin addinin ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta bar matatar Dangote ta sayar da man fetur ga ƴan kasuwa kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng