Gwamna Uba Sani Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya kan Matsalar Tsaro, Ya Ba da Shawara
- Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya taɓo batun matsalolin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar nan
- Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen matsalolin nan ba da jimawa ba
- Ya buƙaci al'ummar jihar Kaduna da su ci gaba da yiwa shugabanni addu'o'i domin Allah ya ba su ikon shawo kan matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan matsalolin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar nan.
Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnati tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Gwamna Uba Sani ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin wani taron addu'o'i na musamman na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Uba Sani ya ba da?
Sai dai ya bukaci ƴan Najeriya da su kasance masu kishin ƙasa, yana mai cewa ba su da wata ƙasa wacce ta wuce Najeriya.
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Dr. Abdulkadir Muazu Meyere ya wakilta, ya tabbatar da cewa ƙalubalen tattalin arziƙi da tsaro da ke addabar ƙasar nan sun kusa zama tarihi.
"Muna tabbatarwa ƴan Najeriya cewa, gwamnati na aiki tuƙuru domin shawo kan ƙalubalen da tattalin arzikin ƙasar nan ke fuskanta da kuma matsalolin tsaro."
"A matsayinmu na ƴan Najeriya, mu sani cewa, ba mu da wata ƙasa sai Najeriya, domin haka dole ne mu gina ƙasar mu sannan gina ƙasa ya fara ne daga son ƙasarmu da kuma kishin ƙasa."
- Gwamna Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya kuma yi kira ga al’ummar Kaduna da su ci gaba da yiwa Najeriya addu’a da shugabanni a matakin ƙasa da jiha, domin Allah ya kawo sauƙin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.
PDP ta samu cikas a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam'iyyar PDP ta samu koma baya a jihar Kaduna bayan da magoya bayan Sanata Shehu Sani suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Mutane 10,000 daga cikin magoya bayan tsohon sanatan suka koma APC a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba bayan nada shugabannin PDP na Kaduna.
Asali: Legit.ng