26 Oktoba: KANSIEC Ta Jaddada Ranar Gudanar da Zaben Kano duk da 'Hukuncin Kotu'

26 Oktoba: KANSIEC Ta Jaddada Ranar Gudanar da Zaben Kano duk da 'Hukuncin Kotu'

  • Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) ta yi watsi da wani hukuncin kotu da ke haramta mata shirya zabe
  • Daraktan yada labaran hukumar, Bashir Habib Yahaya ya shaidawa Legit cewa takardar bogi ce, kuma ba za ta hana gudanar da zabe ba
  • Bashir Habib Yahaya ya shawarci masu sha'awar tsayawa takara su gaggauta sayen fom kafin a rufe a yau, ranar 26 Oktoba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta Kano ta yi watsi da takardar da wasu yan siyasa ke yadawa na cewa kotu ta dakatar da gudanar da zabukan kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

'Babu gudu babu ja da baya' APC ta fadi yadda za ta gwabza da NNPP a zaben Kano

Daraktan yada labarai na hukumar, Bashir Habibu Yahaya ne ya shaidawa Legit hakan a yau biyo bayan wata takarda da ke yawo a kan cewa kotu ta dakatar da gudanar da zaben.

KANSIEC
KANSIEC ta jaddada ranar zaben kananan hukumomi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bashir ya bayyana cewa yancin jama'a ne su gudanar da zaben kananan hukumomi, kuma mafi yawan jihohin kasar nan sun gudanar da zabensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KANSIEC za ta gudanar da zabe a Kano

Daraktan yada labaran hukumar zabe ta KANSIEC, Bashir Habibu Yahaya za ta ci gaba da shirin gudanar da zabe kamar yadda aka tsayar da gudanar da zaben ranar 26 Oktoba, 2024 tun da fari.

Bashir Habibu Yahaya ya ce ana gudanar da zabukan kananan hukumomi a dukkanin jihohin kasar nan, saboda haka Kano ba za ta zama bare ba.

Hukumar KANSIEC ta fadi ranar rude sayen fom

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta takawa APC da PDP burki kan zaben Kananan hukumomi da za a yi

Bashir Habib Yahaya ya tabbatar da cewa a yau, 26 Satumba, 2024 ne ranar karshe na sayen fom, saboda haka a shawarci masu sha’awar tsayawa takara su gaggauta sayo fom a bankuna.

Ya kara da cewa babu gudu babu ja ba baya kan shirin gudanar da zaben kananan hukumomi domin tabbatarwa jama'a damarsu ta zabar wanda su ke bukata bisa dokar kasa.

APC na shirin gwabzawa a zaben Kano

A baya mun kawo labarin cewa jam'iyyar APC, reshen jihar Kano ta ce za ta yi tsayin daka wajen tabbatar da ba a yi magudin zabe a zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas ne ya bayyana matsayarsu, inda ya bukaci hukumar zabe ta tabbata ta yi masu adalci tare da bayyana gaskiyar sakamakon zaben.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.