Mahaifiyar Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Sakkwato

Mahaifiyar Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Sakkwato

  • Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban hukumar EFCC ta ƙasa, Abdulrasheed Bawa rasuwa ranar Laraba da daddare
  • Hajiya Hadiza Ahmed Bawa ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a asibitin koyarwa na jami'ar Usman Ɗanfodio
  • Bayanai sun nuna za a maida ita garin Jega a jihar Kebbi domin yi mata janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya rasa mahaifiyarsa.

Hajiya Hadiza Ahmed Bawa ta riga mu gidan gaskiya ne a jihar Sakkwato ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024 da daddare.

Abdulraheed Bawa.
Allah ya yiwa mahaifiyar tsohon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa rasuwa Hoto: EFCC
Asali: UGC

Har yanzun babu cikakken bayanin kan rasuwar mahaifiyar Abdulrasheed Bawa amma wata majiya daga EFCC ta tabbatar da lamarin ga Daily Trust.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu, ta tabbatar da naɗin CJN a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyar Bawa ta rasu a asibitin UDUTH

Hajiya Hadiza ta rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Usman Ɗan Fodio da ke Sakkwato (UDUTH)

Bayanai sun nuna cewa za a yi jana'izar marigayiyar a Jega da ke jihar Kebbi da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

"Ta rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Usman Ɗan Fodio UDUTH da ke Sokoto kuma za a yi jana’izarta a Jega, Kebbi insha Allah da misalin karfe 2:30 na rana," in ji majiya. 

Legit Hausa ta fahimci cewa ana shirin ɗaukar gawar mamaciyar zuwa jihar Kebbi, inda za a yi mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada ranar Alhamis.

Yadda Bawa ya zama shugaban EFCC

Bawa, farar hula na farko da ya zama shugabanci EFCC, an nada shi a matsayin shugaban hukumar a ranar 16 ga Fabrairu, 2021, kuma majalisa ta amince da shi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya fara rabawa waɗanda ambaliya ta shafa kuɗi da kayan abinci

Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi daga aiki a watan Yuli, 2023 bayan ya karɓi mulki daga Muhammadu Buhari.

EFCC ta yi magana kan Yahaya Bello

A wani rahoton hukumar EFCC ta bayyana dalilan da ya sa ta ki sauraron tsohonɓgwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello lokacin da ya miƙa kansa a makon jiya.

A wata sanarwa da ta fitar, EFCC ta ce ta gano cewa Bello ya yi wani shiri kuma ya zo tare da gwamna mai mai rigar kariya da muƙarrabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262