"Sai Ka Gurfana a gaban Kotu:" Hukumar EFCC Ta Kalubalanci Yahaya Bello

"Sai Ka Gurfana a gaban Kotu:" Hukumar EFCC Ta Kalubalanci Yahaya Bello

  • Bayan neman mafaka a kotun koli, hukumar EFCC ta bayyana cewa dole tsohon gwamnan Kogi kotu ya gurfana a kuliya
  • A ranar Laraba ne lauyan Yahaya Bello ya shaidawa kotun Mai Shari'a Emeka Nwite cewa sun shigar da kara kotun koli
  • Amma a martaninta, hukumar EFCC ta bakin kakakinta, Dele Oyewale ta ce sun gama hada shaidu kan zargin badakalarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce a shirye ta ke wajen fuskantar tsohon gwamnan Kogi, Bello Yahaya a kotu.

Hukumar EFCC na zargin tsohon gwamnan da wawashe kudin al'umar jiharsa da yawansu ya kai Naira biliyan 80.2.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

Yahaya
EFCC ta ce dole tsohon gwamnan kogi ya gurfana gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Jaridar The Nation Tribune ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na EFCC, Dele Oyewale ya ce dole sai Yahaya Bello ya fuskanci alkali kan zargin da ake yi masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta sako Yahaya Bello a gaba

Jaridar Nigerian ta wallafa cewa kamar yadda aka gurfanar da tsofaffin ministoci, gwamnoni da manyan jami'an gwamnati kan zargin almundahana, dole Yahaya Bello ma ya gurfana a kotu.

Ya ce tun da tsohon gwamnan ya ki mutunta gayyatar da EFCC ta rika yi masa, zai yi jawabi a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya.

"Mun tara shaidu kan Yahaya Bello:" EFCC

Hukumar EFCC ta bayyana cewa tuni ta kammala hada kwararan shaidu kan zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Jami'in hulda da jama'a na EFCC, Dele Oyewale ya ce da zarar an fara zaman shari'ar Yahaya Bello, za a zakulo shaidun da aka tara sannu a hankali.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya gaji da matsin lambar EFCC, ya roƙi Tinubu Alfarma

EFCC vs Yahaya: Kotu ta dage shari'a

A baya mun wallafa cewa babbar kotun tarayya karkashin Mai Shari'a Emeka Nwite ta dage zaman shari'ar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello bisa zargin almundahana.

Gwamnatin tarayya na tuhumar tsohon gwamnan da yashe asusun gwamnatin Kogi a zamanin ya na gwamna, inda EFCC ta ce ya wawashe Naira biliyan 80.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.