An Firgita da Jin Harbe Harbe da EFCC Suka Farmaki Yahaya Bello a Abuja
- An shiga firgici bayan jin karar harbe-harbe da ake zaton naEFCC ne a kokarin cafke tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ana zaton jami'an hukumar EFCC ne ke harbin a kokarin cafke tsohon gwamnan a Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan shafe tsawon lokaci hukumar na neman Yahaya Bello kan karkatar da makudan kudi har N80.2bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Dambarwa tsakanin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da Hukumar EFCC ta dauki sabon salo a birnin Abuja.
Da daren yau Laraba 18 ga watan Satumbar 2024 aka yi ta jin karar harbe-harbe a gidan saukar baki na gwamnatin jihar Kogi.
EFCC ta kai samame kan Yahaya Bello
Leadership ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta sake kai samame domin cafke tsohon gwamnan kan zargin badakalar kudi da yake ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Ohiare Michael ya ce jami'an EFCC sun mamaye gidan da Yahaya Bello yake da daren yau Laraba.
"Suna ta harbe-harbe ta ko ina yayin da suka mamaye gidan da Yahaya Bello ya ke."
- Ohiare Michael
Hukumar tana zargin Yahaya Bello da karkatar da makudan kudi har N80.2bn yayin da yake mulkin jihar, cewar rahoton The Guardian.
Da gaske Yahaya Bello ya mika kansa?
Tun farko an yi ta yada jita-jita cewa Yahaya Bello ya mika kansa ga hukumar EFCC da ke nemansa ruwa a jallo.
Rahotanni suka ce tsohon gwamnan ya mika wuya ne a yau Laraba 18 ga watan Satumbar 2024 a ofishin hukumar da ke Abuja.
Har ila yau, hadimin tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa Yahaya Bello ya ziyarci ofishin hukumar amma ba su yi masa tambayoyi ba.
EFCC ta yi magana kan Yahaya Bello
Kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ta yi magana kan dambarwar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da ake ciki.
Hukumar ta ƙaryata cewa Yahaya Bello ya mika kansa gare ta inda ta ce tana nemansa ruwa a jallo har zuwa wannan lokaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng