Borno: Manya na Ci Gaba da Zuwa Jaje Maiduguri, An Kara Bada Tallafin N50m
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ziyarci jihar Borno domin jajantawa waɗanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su
- Sanata Ahmad Lawan ya kuma ba da tallafin N50m ga waɗanda ibtla'in ya shafa tare da addu'ar Allah ya ji kan waɗanda suka rasu
- Ya kuma yi kira ga kungiyoyin agaji su taimakawa jihar Borno wajen daƙile illar da ka iya biyo bayan ambaliyar ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bada gudunmuwar Naira miliyan 50 don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.
Sanata Ahmad Lawan ya ba da wannan tallafi ne a lokacin da ya kai ziyara Maiduguri domin jajantawa Gwamna Babagana Umaru Zulum ranar Talata.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo ya fitar a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmad Lawan ya je jaje Maiduguri
Sanata Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa, ya kai ziyara Maiduguri ne tare da rakiyar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Rt. Hon. Yau Usman Dachia.
Sauran waɗanda suka raka Ahmad Lawal sun haɗa da ƴan majalisar jiha biyu, mai ba da shawara kan kasafin kudi, Alhaji Suleiman Jamo da wasu masu ruwa da tsaki.
Sanata Lawan ya yabawa gwamnan Borno
Da yake jawabi, Ahmad Lawan ya yabawa Gwamna Zulum da gwamnatin jihar Borno kan yadda suka dauki matakin gaggawa a lokacin da ruwa ya fara ambaliya.
Ya ce gwamna da muƙarrabansa sun cancanci yabo kan yadda suka tura jami’an agaji da kwashe mutanen da ibtila'in ya rutsa da su, in ji Channels tv.
Bugu da ƙari, Ahmad Lawal ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa tallafi, goyon baya da matakin taimakawa mutane da ta ɗauka cikin gaggawa.
Haka nan kuma ya bukaci abokan aiki da kungiyoyin agaji da su taimakawa jihar Borno domin dakile illar ambaliyar ruwan.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka rasu, kuma Allah ya tashi kafaɗun waɗanda suka raunata sakamakon ibtila'in.
Majalisa dattawa ta tura tawaga Maiduguri
A wani rahoton kuma majalisar dattawan kasar nan ta aika tawaga ta musamman zuwa Borno domin jajanta wa gwamna Babagana Zulum kan ambaliya.
Har yanzu jama'a na cikin mawuyacin hali bayan ruwa ya haura madatsar Alau, ya kuma mamaye gidaje, hanyoyi da sauran wurare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng