Ana Jimamin Ambaliyar Ruwa, Gwamna Zulum Ya Gargadi Sarakunan Borno
- Gwamnan jihar Borno ya gargaɗi sarakunan gargajiya kan illar da ke tattare da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba
- Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa idan ba a yi taka tsan-tsan ba lamarin zai iya zama gagarumar matsalar rashin tsaro
- Zulum ya yi gargaɗin cewa idan sarakunan suka bari aka ci gaba da haƙar ma'adanan, nan da ƴan shekaru sai sun rasa kasar noma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiya a Kudancin Borno.
Gwamna Zulum ya gargaɗi sarakunan ne kan illolin da ke tattare da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a cikin yankunansu.
Gwamna Zulum ya gargaɗi sarakuna
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Zulum ya nunawa sarakunan illar hakan ne domin ka da lamarin ya rikiɗe ya haifar da matsalar rashin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi wannan gargaɗin a ranar Laraba lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Kudancin Borno a ziyarar jaje da suka kawo masa sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku.
Gwamna Zulum ya ce Borno ta yi fama da rikice-rikice da dama kuma ba za ta amince da duk wani abu da zai iya sake kawo wani rikici a jihar ba.
Wace shawara Zulum ya ba da?
"Alhamdulillah an rage kaso 95% cikin 100% na hare-haren Boko Haram a Borno amma idan ba mu shawo kan haƙar ma’adanai a yankunan ba, zai riƙide zuwa tada ƙayar baya."
"Ka da mu ɗauki batun haƙar ma’adanai da wasa. Ya kamata sarakuna, masu riƙe da sarautun gargajiya su yi hattara da shi."
"Ku manta da ƴan kuɗin da matanmu da yaranmu suke samu daga ayyukan haƙar ma’adinai."
"Idan kuka bari aka ci gaba da haƙar ma’adanai a waɗannan wuraren, to ba za ku samu wuraren da za ku yi noma ba a cikin shekaru 10 masu zuwa. Mu ƙara dagewa da addu’o’in Allah ya kiyaye faruwar wani abu mara kyau ga al’ummarmu."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Gwamna ya yi gaskiya
Wani ɗan Kudancin Borno mai suna Aliyu Biu ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas gargaɗin da gwamnan ya yi abu ne mai kyau domin idan ba a yi taka tsan-tsan ba lamarin na iya riƙidewa ya zama wani abu daban.
"Jihar Zamfara ma da haka abin ya fara gashi nan yanzu ya zama wani abu babba. Tabbas ya kamata a ƙara sanya idanu kan lamarin."
- Aliyu Biu
Sanatoci sun je jaje a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar yan majalisar dattawa ta ziyarci gidan gwamnatin jihar Borno domin jajanta wa jama'ar Maiduguri bisa mummunan iftila'in ambaliya.
Mataimakin shugaban majalisar, Barau I Jibrin ne ya jagoranci tawagar, inda ya bayyana cewa su na sane da girman iftila'in da mawuyacin halin da ya jefa jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng