Ana Jimamin Ambaliyar Ruwa, Gini Ya Rufto kan Daliban Jami'a

Ana Jimamin Ambaliyar Ruwa, Gini Ya Rufto kan Daliban Jami'a

  • Wani ginin bene mai hawa uku ya rufto kan jami'an ɗalibar Benin (UNIBEN) a ranar Asabar, 14 ga watan Satumban 2024
  • Ginin wanda ya rufto a unguwar Ekosodin wacce ke makwabtaka da jami'ar ya ritsa da ɗalibai masu yawa waɗanda suka maƙale
  • An samu nasarar ceto wasu daga cikin ɗaliban da lamarin ya ritsa da su yayin da ake ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ragowar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Wasu ɗalibai sun makale a yayin da wani bene mai hawa uku ya rufta sakamakon ruwan sama a unguwar Ekosodin da ke birnin Benin a jihar Edo.

Unguwar Ekosodin, wacce ke da iyaka da jami'ar Benin (UNIBEN), tana da ɗalibai masu yawa da ke zaune a cikinta.

Kara karanta wannan

Kasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya turo saƙo kan harajin N50m da ya sa a Zamfara

Gini ya rufto a Edo
Gini ya rufto kan jami'ar UNIBEN Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutane da dama sun samu raunuka sakamakon ruftawar ginin da ke kan titin Ekhator.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gini ya rufto kan ɗalibai

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an ceto wasu daga cikin ɗaliban da suka makale yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran.

Wasu ɗaliban da suka nemi a sakaya sunansu, sun shaidawa manema labarai cewa, tawagar jami’an ceto na jami’ar sun yi nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da suka maƙale, duk da cewa wasu da dama sun samu munanan raunuka.

Sun bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran da suka maƙale a ginin.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Hukumomin jami’ar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari babban asibiti, sun yi awon gaba da mata a Arewa

A lokacin da aka tuntuɓi hukumar kashe gobara ta jihar, wani jami’i ya ce jami'an hukumar suna wajen domin su taimaka a aikin ceto ɗaliban.

Gini ya rufto a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani sashe na wani bene mai hawa biyu ya rufta a Abuja da safiyar Asabar, inda mutane da dama suka makale a cikin ɓaraguzan ginin.

Ginin wanda ke kusa da shahararren otal din Cupid da ke kan titin Cupid (Sultan Dasuki Way) a Kubwa a baya wani otal ne mai suna Al-Hilal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng