Ambaliyar Ruwa: Gwamna Zulum Ya Fadi Babbar Damuwarsa

Ambaliyar Ruwa: Gwamna Zulum Ya Fadi Babbar Damuwarsa

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna damuwarsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar
  • Gwamna Zulum ya bayyana cewa ya damu matuƙa kan yiwuwar wasu shugabannin Boko Haram sun tsere daga gidan yari
  • Ambaliyar ruwan dai wacce ta auku a jihar ta jawo asarar rayuwa da dukiyoyi na miliyoyin Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana babbar damuwar da yake da ita kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar.

Gwamna Zulum ya ce ya damu matuƙa da yadda wasu shugabannin ƙungiyar Boko Haram da ke zaman gidan yari suka tsere daga gidan yarin da ke Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwan.

Kara karanta wannan

'Akwai ƙarancin abinci:' Zulum ya fadi halin da ake ciki kwanaki 3 da ambaliya

Zulum ya damu kan ambaliyar ruwa
Zulum ya damu kan yiwuwar tserewar shugabannin Boko Haram Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Ambaliya ta yi ɓarna a Borno

Jaridar Daily Trust ta ce ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira a birnin Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa, ambaliyar ta kuma lalata wani ɓangare na tsohon gidan yarin inda aka kwashe fursunoni da dama zuwa sabon gidan yarin mai cikakken tsaro a birnin Maiduguri.

Akwai rahotanni dai masu cewa an kwashe wasu fursunonin, kuma wasu daga cikinsu sun tsere.

Me Zulum ya ce kan ambaliyar ruwa?

Da aka tambaye shi a wata hira da BBC Hausa, ko ya damu cewa wasu shugabannin Boko Haram sun tsere, Gwamna Zulum ya nuna damuwarsa kan hakan.

"Na damu, eh, na damu matuƙa. Amma kuma ku tuna cewa gwamnatin jihar Borno ta samar da shirin gyara tarbiyyar masu tada ƙayar baya wanda ya ba su damar tuba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ta turawa gwamnoni sama da N100bn bayan abin da ya faru a Maiduguri

"A cikin shekaru biyun da suka gabata, sama da ƴan Boko Haram 200,000 da iyalansu suka tuba, kuma ina ganin hakan ya haifar da kyakkyawan sakamako wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Borno."

- Farfesa Babagana Umara Zulum

An ceto mutane a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayyana ceto mutane 3,682 da ambaliyar ruwa ta tare a jihar Borno.

Shugaban hukumar agajin Borno, Barkindo Mohammed ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Juma'a, inda ya ke bayani kan halin da ake ciki a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng