Ambaliyar Ruwa: Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar da Rabon Kayan Tallafi
- Gwamnan jihar Jigawa, Mai girma Umar Namadi ya waiwayi mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a daminar nan
- Gwamnan ya amince a fitar da N315.5m domin rabawa ga mutane 15,775 da ke a sansanonin ƴan gudun hijira a inda lamarin ya shafa
- Namadi ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da tallafi ga mutanen tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Gwamna Umar Namadi ya amince da fitar da N315.5m ga mutane 15,775 da suke a sansanonin ƴan gudun hijira a cikin ƙananan hukumomi 20 da ambaliyar ta shafa.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa.
Gwamna Namadi ya ba da tallafin ambaliya
Gwamnan wanda ya je ƙaddamar da rabon kayayyakin tallafi ga mutanen ya bayyana cewa za a ba da tallafin kuɗin ne da abinci domin rage raɗaɗin da suka fuskanta sakamakon ambaliyar ruwan, rahoton Leadership ya tabbatar.
Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ta damu da mutanen da lamarin ya shafa tun farkon faruwar ambaliyar ruwan kuma za ta ci gaba da ba su tallafi tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya.
"Yau muna ƙaddamar da raba buhun masara, shinkafa da dawa mai nauyin kilo 10, kwalin taliya da tsabar kuɗi N20,000 ga kowane daga cikin mutane 15,775 da ambaliyar ruwan ta shafa."
"A yayin da muke ta'aziyyar mutane 36 da suka rasu sakamakon ambaliyar ruwan da jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka rasa gonakinsu, za mu ci gaba da ba da tallafi domin rage raɗaɗin da mutane ke fuskanta."
- Gwamna Umar Namadi
Minista ya ba gwamnatin Jigawa tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro Mohammed Badaru ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Jigawa.
Ministan ya ba da tallafin N20m ga gwamnatin jihar Jigawa a ƙoƙarin da take na tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng