Ambaliya: Mutane Kusan 50 Sun Rasu, Gidaje 6000 Sun Lalace a Garuruwa 200 a Kano

Ambaliya: Mutane Kusan 50 Sun Rasu, Gidaje 6000 Sun Lalace a Garuruwa 200 a Kano

  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kano ta bayyana cewa mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a sassan jihar
  • Shugaban hukumar a Kano, Isyaku Abdullahi Kubarachi ne ya tabbatar da haka, inda ya ce akalla mutane 29 ne su ka rasu
  • Isyaku Kubarachi ya jajanta wa wadanda iftila'in ya afka masu, inda ya shawarci mutane su daina gini a kan hanyoyin ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta jawo asarar rayuka da dama.

Shugaban hukumar na Kano, Isyaku Abdullahi Kubarachi da ya bayyana haka ya ce kananan hukumomi 27 ne iftila'in ya afka masu.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa Akpabio ya kadu da ambaliya a jihohin Arewa, ya sha alwashi

Ambaliya
Mutane 49 sun rasu sakamakon ambaliya a Kano Hoto: Mallam Abba Zaria
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa mutane 49 ne aka tabbatar da rasuwarsu a garuruwa 226 a kananan hukumomi 27 daga cikin 22 na jihar Kano.

Kano: Kananan hukumomin da aka yi ambaliya

Wasu daga cikin kananan hukumomin da aka yi ambaliya sun hada da Tudun Wada, Gwale, Wudil, Danbatta, Ajingi, Dala, Gwarzo, Madobi, Bichi, Kano Municipal da Karaye.

Leadership ta wallafa cewa sauran garuruwan sun hada da Tarauni, Minjibir, Bebeji, Rogo, Shanono, Kabo, Garin Malam da Ungogo.

Ragowar su ne Kumbotso, Nasarawa, Kura, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Gezawa, Rogo da Bagwai.

Ambaliya ta lalata gidaje da gonaki

Shugaban hukumar SEMA na Kano, Isyaku Abdullahi Kubarachi ya ce ambaliya ta lalata gidaje akalla 6,583 inda ta shafi mutane 38,814 da a yanzu haka ke bukatar tallafi.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

Ambaliyar ta lalata gonaki 8,289 wanda ya kai kadada 36,265, sannan mutane 1,414 ne su ka rasa muhallansu, kuma mutane 139 sun jikkata, inda gwamnati ke koarin taimaka masu.

Ana fargabar ambaliya a Yobe

A wani labarin mun ruwaito cewa gwamnatin Yobe ta gargadi mazauna kananan hukumomu tara a jihar na cikin barazanar ambaliya saboda cikar wasu madatsun ruwa.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, Dr. Mohammed Goje ya bayyana cewa yanzu haka ana cikin shirye-shiryen tunkarar ambaliya ta hanyar jibge jami'ai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.