A Kwana da Shiri: Ana Fama da Ambaliya a Borno, NiMET Ta Yi Hasashe Mai Firgitarwa
- Yayin da al'ummar Borno ke fama da matsalar ambaliya da ta nemi shafe Maiduguri, hukumar hasashen yanayi (NIMET) ta yi sabon hasashe
- A sabon hasashen, NIMET ta bayyana cewa za a samu mamakon ruwa kamar da bakin kwarya hadi da tsawa na kwanaki uku a jere
- Jihohin da NIMET ta bayyana cewa za a samu ruwa da tsawa sun hada da Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa (Nimet) ta gargadi mazauna kasar nan da cewa za a samu mamakon ruwan sama hadi da tsawa daga ranar Laraba zuwa Juma'a.
Hukumar ta fitar da sabon hasashen ne yayin da jama'ar Maiduguri a jihar Borno da wani sashe na Bauchi ke fama da matsananciyar ambaliya.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wasu daga cikin jihohin Arewa da su ka hada da Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da Kaduna za su fuskanci ruwa da tsawa a safiyar Laraba.
Jihohin da za a fuskanci mamakon ruwa
Sauran jihohin da NiMET ta yi hasashen ruwa kamar da bakin kwarya sun hada da wasu sassan Kano, Borno, Katsina, Adamawa, Kaduna, Taraba, Zamfara, Kebbi, da Jigawa.
A yankin Arewa ta Tsakiya kuma akwai jihohin Nasarawa, Neja, Binuwai, Kogi, Kwara da Abuja, yayin da ake tsammanin ruwan a Kudanci a jihohin Oyo, da Osun.
Sauran jihohin sun hada da Ekiti, Ogun, Ondo, Lagos, Edo, Delta, Cross River da Akwa Ibom, kamar yadda Solacebase ta wallafa.
Ambaliyar ruwa: NiMET ta bayar da shawarwari
Hukumar NiMET ta shawarci jama'a su dauki matakan kare kawunansu yayin da ake sa ran afkuwar ambaliyar ruwa.
NiMET ta ce ana sa ran za a samu iska mai karfi gabanin mamakon ruwan sama, wanda haka ne zai iya kara ta'azzara lamarin.
Ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri
A baya kun ji cewa madatsar ruwan Alo ta balle a Maiduguri wanda ya jawo ambaliya mafi muni da aka gani a jihar Borno a shekaru 30, inda ruwan ya mamaye gidaje da sauran wurare.
Ambaliyar ta jawo matsaloli da dama inda jami'an lafiya su ka shiga fargabar akwai yiwuwar a samu ballewar cututtuka bayan ruwan ya wanke makabartu da gidan namun daji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng