'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari da Asuba, Sun Kashe Bayin Allah a Arewa

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari da Asuba, Sun Kashe Bayin Allah a Arewa

  • Ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki garin Naka, hedkwatar ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benuwai
  • Wani ganau ya shaida cewa maharan sun kutsa cikin garin da misalin karfe 4:00 na asuba, suka buɗewa mutane wuta
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Benuwai, SP Cathrine Anene ta ce rahoton harin bai isa ofishinta ba amma za ta bincika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Wasu ‘yan bindiga a safiyar ranar Talata sun kashe mutane bakwai a garin Naka, hedikwatar karamar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benuwai.

Garin Naka dai yana kan babban titin tarayya wanda ya taso daga Makurdi ya ratsa ta Naka, Adoka har zuwa Ankpa a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Jami'an agaji sun maƙale a ruwa daga zuwa ceto mutane

Gwamna Alia na jihar Benuwai.
Yan bindiga sun kashe mutum 7 a hedkwatar ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benuwai Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa galibin mazauna garin Naka manoma ne kuma sama da shekaru 16 da suka wuce garin ke fama da hare-haren da ake zargin makiyaya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka yi ta'adi

Wani ganau, Terna Ukaa ya shaidawa manema labarai cewa ƴan bindigar sun faramki garin da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin yau Talata.

Ya ce maharan sun shiga garin ta hanyar Adoka kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mutane, waɗanda mafi akasari suna kwanceba su tashi daga barci ba.

Ukaa ya ce ba su dauki komai ba a harin, inda ya ƙara da cewa ga dukkan alamu yan bindigar sun zo ne da niyyar kisa kawai.

Makiyaya sun lalata gonakin manoma

A cewarsa, kafin wannan harin na ranar Talata, wasu makiyaya ɗauke da makamai sun lalata gonakin mazauna garin Naka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari wani asibiti a Kaduna, sun tafka ɓarna

Mista Terna Ukaa ya ce makiyayan sun yi amfani da shanu, waɗanda suka shiga gonakin rogo, shinƙafa da gero, suka cinyewa mutane amfanin gona.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton tabbacin faruwar lamarin ba, amma ta yi alƙawarin za ta bincika.

Yan bindiga sun farmaki asibiti a Kaduna

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun shiga wani karamin asibiti a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna ranar Litinin.

Shugaban rundunar ƴan banga na yankin ya ce maharan sun fara shiga wata maƙarantar sakandire kafin daga bisani su shiga asibitin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262