Malami Ya Gayawa Tinubu Kuskuren da Yake Yi kan Tabarbarewar Tattalin Arzikin Najeriya

Malami Ya Gayawa Tinubu Kuskuren da Yake Yi kan Tabarbarewar Tattalin Arzikin Najeriya

  • Primate Babatunde Elijah Ayodele ya caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan yadda yake kashe kuɗi a gwamnatinsa
  • Babban faston ya bayyana cewa ɓarnar kuɗin da Shugaba Tinubu ke yi na ƙarar taɓarɓarar da tattalin arziƙin ƙasar nan
  • Ya bayyana cewa ya kamata shugaban ƙasan ya rage kashe kuɗi a gwamnatinsa sannan ya mayar da hankali wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya sake caccakar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Fasto Ayodele ya soki Shugaba Tinubu ne kan yadda yake kashe kuɗi a gwamnatinsa duk da halin taɓarɓarewar tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya gayawa Shugaba Tinubu gaskiya kan tsadar rayuwa

Fasto Ayodele ya caccaki Tinubu
Primate Ayodele ya ba Tinubu shawara Hoto: @PrimateAyodele, @DOlusegun
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya fitar.

Me Ayodele ya ce kan gwamnatin Tinubu?

Fasto Ayodele ya zargi gwamnatin Tinubu da ba da fifiko wajen siyo kayayyakin alatu maimakon farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Ya yi nuni da cewa tattalin arziƙin ƙasar nan ba zai farfaɗo ba idan har gwamnatin Tinubu ta ci gaba da wannan ɗabi'ar.

"Shugaba Tinubu na ci gaba da lalata tattalin arziƙin Najeriya maimakon ya nemo hanyoyin farfaɗo da shi. Yawan kashe kuɗin da ba su kamata bai taimakon ƙasar nan."
"A wasu lokutan ina mamakin cewa waɗannan jami'an gwamnatin ba su sun halin da ake ciki ba, domin da sun sani da ba su riƙa siyo wasu abubuwan ba a wannan lokacin."

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: 'Yan Najeriya sun yi martani kan ajiye aikin hadimin Tinubu

"Ba na tunanin tattalin arziƙin mu zai farfaɗo a 2025, ya kamata gwamnati ta rage kashe kuɗi, gwamnati tana kashe tattalin arziƙi da wannan ɓarnar kuɗin da take yi. Ƴan Najeriya na cikin wuya amma gwamnati na nuna kamar ba ta damu ba."

- Primate Babatunde Elijah Ayodele

Tinubu zai kori wasu ministoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai yiwuwar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul.

Wata majiya mai tushe a fadar shugaban ƙasa ta ce garambawul ɗin za a yi shi ne domin a kawo sababbin fuskokin da za su ƙara ɗaga darajar gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng