Tinubu Ya Shirya Yiwa Majalisar Ministoci Garambawul, Za a Runtuma Kora

Tinubu Ya Shirya Yiwa Majalisar Ministoci Garambawul, Za a Runtuma Kora

  • Alamu na nuna cewa wasu daga cikin monistocin da ke cikin gwamanatin Shugaba Bola Tinubi za su rasa kujerunsu
  • Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya shirya tsaf domin yiwa majalisar ministocinsa garambawul
  • Majiyar ta nuna cewa shugaban ƙasan bai gamsu da kamun ludayin wasu daga cikin ministocin ba kuma a shirye yake ya kore su daga muƙamin su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Akwai yiwuwar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul.

Idan ba wani sauyi aka samu ba, Shugaba Tinubu zai yi garambawul ɗin ne a cikin sati mai zuwa.

Tinubu zai kori ministoci
Akwai yiwuwar Tinubu ya kori wasi ministoci Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta rahoto cewa wata majiya mai tushe a fadar shugaban ƙasa ta ce garambawul ɗin za a yi shi ne domin a kawo sababbin fuskokin da za su ƙara ɗaga darajar gwamnati.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya gayawa Shugaba Tinubu gaskiya kan tsadar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Tinubu zai yi garambawul?

Majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar Tinubu ya yi garambawul ɗin kafin ya tafin taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) wanda za a yi a birnin New York a cikin sati mai zuwa.

Majiyar ta ce Shugaba Tinubu yana sane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi na rashin kataɓus ɗin wasu ministocinsa kuma a shirya yake ya sallame su.

Majalisar ta ƙara da cewa an kammala haɗa jerin sunayen ministocin da za a kora daga gwamnatin.

"Shugaba Tinubu bai gamsu da kataɓus ɗin wasu daga cikin ministocinsa ba kuma a shirye yake ya sallame su."
"Bayan ya dawo daga taron UNGA, shugaban ƙasa zai kafa sabuwar majalisar ministoci."

- Wata majiya

Jaridar ta ƙara da cewa wani tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari na daga cikin waɗanda ake sa ran ba muƙamin minista.

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: Kura kurai 2 da suka sa hadimin Tinubu ya ajiye aikinsa

Jigo a APC ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara.

Olatunbosun Oyintiloye ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cire ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ciki.

Olatunbosun Oyintiloye ya nuna cewa ƴan Najeriya na shan wuya wanda hakan ya sanya dole shugaban ƙasan ya ɗauki matakan kawo musu ɗauki

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng