Ajuri Ngelale: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani kan Ajiye Aikin Hadimin Tinubu

Ajuri Ngelale: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani kan Ajiye Aikin Hadimin Tinubu

  • Ƴan Najeriya na ci gaba da martani kan murabus ɗin da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya yi
  • Yayin da wasu suka yi masa fatan Allah ya ba iyalansa lafiya, wasu sun danganta murabus ɗin nasa kan gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Ajuri Ngelale ya sanar da murabus ɗin nasa ne a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, inda ya danganta hakan kan matsalar rashin lafiyar iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan Najeriya sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan murabus ɗin Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, Ngelale ya yi murabus daga muƙaminsa na mai ba Shugaba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai.

Kara karanta wannan

Babban hadimin Shugaba Tinubu ya ajiye aikinsa, ya jero dalilai masu ƙarfi

Ajuri Ngelale ya ajiye aiki
Ajuri Ngelale ya tafi hutu daga aikinsa Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Ngelale yayi murabus daga gwamnatin Tinubu

Hadimin na Tinubu ya bayyana cewa zai je hutun aiki na sai baba ta gani sakamakon wani ƙalubale da yake fuskanta a cikin iyalansa na rashin lafiya.

Ya bayyana cewa a shirye yake ya dawo bakin aikinsa duk lokacin da damar hakan ta samu.

Martanin ƴan Najeriya kan murabus ɗin Ngelale

Sai dai ƴan Najeriya musamman masu faɗa a ji sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da murabus ɗin Ajuri Ngelale.

Ga wasu daga cikinsu nan a ƙasa:

Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar, jigo a jam’iyyar PDP ya ce Ngelale ya yi murabus ne saboda halin da ƙasar nan ke ciki.

Ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

"Ajuri Ngelale kawai ya gaji da gayawa ƴan Najeriya tatsuniya ne."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi dalilin 'yan bindiga na daukar makamai

A wani ributu da ta yi a shafinta na X, Rinsola Abiola, hadimar Shugaba Tinubu, ta jajanta masa tare da yin addu'ar Allah ya ba iyalansa lafiya.

"Tunanina da addu'o'i na suna tare da ɗan uwana kuma babban abokin aiki, Cif Ajuri Ngelale, yayin da ya tafi hutu daga hidimtawa ƙasar mu domin mayar da hankali kan batun iyalansa da ke buƙatar kulawarsa."

- Rinsola Abiola

Michael Chibuzo ya yi addu'a ga hadimin na Tinubu a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

"Cif Ajuri Ngelale, za a yi kewarka sosai. Allah ya taimake ka yayin da kake fuskantar wannan ƙalubalen a cikin iyalanla. @AjuriNgelale, ina yi maka fatan alheri kan abin da ka sanya a gaba."

- Michael Chibuzo

Nasarorin ziyarar Tinubu a China

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana irin nasarorin da ya samu yayin ziyararsa a kasar China.

Shugaba Tinubu ya ce sun sanya hannun a yarjejeniya da Shugaba Xi Jinping wurin inganta tattalin arziki da sauran lamura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng