Wani Jirgi da Ya Ɗauko Ƴan Kasuwa Ya Gamu da Hatsari, Mutum 4 Sun Rasu a Arewa
- Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum hudu, wasu mutum biyu sun ɓace a yankin ƙaramar hukumar Lafia a jihar Nasarawa
- Rahoto ya nuna kwale-kwalen ya ɗauko ƴan kasuwa akalla 25 da kayayyaki a lokacin da ya nutse a kusa da ƙauyen Ashangwa
- Kantoman da ke kula da Lafiya ta Gabas, Barista Haruna Muhammad ya ce sun fara bincike domin a gano musabbabin hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Mutum hudu sun mutu yayin da wasu biyu suka bace a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a kogin Alogani da ke karamar hukumar Lafiya a Nasarawa.
Rahotanni sun bayyana cewa kwale-kwalen ya ɗauko fasinjoji da tulin kayayyaki a lokacin da ya gamu da hatsarin a hanyar zuwa Ashangwa.
Rahoton Leadership ya nuna cewa hatsarin ya auku ne a ranar da kasuwar yankin take ci kuma an tabbatar da rasuwar fasinjoji huɗu.
Menene ya haddasa kifewar jirgin ruwan?
An tattaro cewa fasinjoji 25 da babura takwas da buhunan kankana hudu ne a cikin jirgin ruwan a lokacin da ya nutse.
Daga cikin mutane 25 da kwale-kwalen ya ɗauko, an yi nasarar ceto 19 da ransu yayin da wasu biyu kuma suka bace, har kawo yanzu ba a gansu ba.
Kantoman ƙaramar hukumar Lafia ta Gabas, Barista Haruna Muhammed ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma aika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan.
Wane mataki mahukunta suka ɗauka?
Ya ce tuni hukumomi suka fara gudanar da bincike domin gano musabbabin nutsewar jirgin ruwan, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Haka zalika Barista Haruna ya ce shugabannin al'umma a yankin sun ɗauko sarkin ruwa da mutanensa domin ceto sauran mutum biyun da kayayyakin da suka nutse.
Legit Hausa ta gano cewa majalisar dokokin jihar Nasarawa ta fara karatu kan dokar kafa hukumar kula da magudan ruwa domin magance faruwar irin haka.
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Bauchi
A wani labarin kun ji cewa wani jirgin kwale-kwale ya samu hatsari a jihar Bauchi inda wasu mutum uku suka ɓace ba a san inda suka yi ba.
Hatsarin jirgin dai ya auku ne a kogin Zindiwa da ke ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi a ranar Asabar, 31 ga watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng