Tashin Fetur: Gwamna Ya Taimakawa Ma'aikata Saboda Tsadar Rayuwa a Najeriya

Tashin Fetur: Gwamna Ya Taimakawa Ma'aikata Saboda Tsadar Rayuwa a Najeriya

  • Gwamnan jihar Ekiti ya kawo sabon tsarin aiki daga gida domin saukakawa ma'aikata saboda halin tsadar rayuwa da ake ciki
  • A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, gwamnan ya rabawa ma'aikata ranakun da za su zauna a gida da waɗanda za su fito aiki
  • Oyebanji ya umarci ma'aikatu su tsara yadda za a tafiyar da sabon tsarin domin ka da ya kawo tangarda a harkokin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya amince ma'aikata su rika zama suna aiki daga gida a wasu kwanakin mako.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin ragewa ma'aikata raɗaɗin wahala da tsadar rayuwar musamman bayan ƙara tashin farashin man fetur.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: An tausayawa ma'aikata, gwamna ya rage kwanakin zuwa aiki

Gwamna Oyebanji.
Gwamna Oyebanji ya ba ma'aikata damar Aiki daga gida saboda tsadar rayuwa a Ekiti Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Twitter

Mai magana da yawun gwamnan, Mr Yinka Oyebode shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya tsara ranakun zama a gida

Sanarwar ta ce Gwamna Oyebanji ya amince ma'aikatan da ke mataki na 1 zuwa 7 su zauna a gida su yi aiki na ranaku uku, ma'ana sau biyu za su fito aiki a mako.

Kazalika ma'aikatan da suka kai mataki na 8 zuwa 12 za su zauna su yi aiki daga gida na kwana biyu, su fito wurin aiki a sauran kwanakin aiki uku.

Sai kuma ma'aikatan da suka kai mataki na 13 zuwa 17 za su yi aiki daga gida na kwana ɗaya, sannan su rika fitowa aiki na sauran ranaku huɗu a mako.

Yaushe sabon tsarin zai fara aiki?

Sabon tsarin zai fara aiki daga ranar Litinin, 9 ga Satumba, 2024, amma ban da ma'aikata masu mahimmanci kamar malamai, ma'aikatan lafiya da sauransu.

Kara karanta wannan

“Hadama ba za ta barsu ba”: Kwankwaso kan hadakar Atiku da ’yan adawa a 2027

Gwamnan ya umarci kowace ma'aikata ta zauna ta tsara jadawalin aiki ta yadda sabon tsarin aiki a gida ba zai kawo tasgaro a ayyukan da gwamnati ta sa a gaba ba.

Oyebanji ya ce za a tafi a wannan tsarin na watanni biyu kuma bayan haka gwamnati za ta sake nazari kafin a ci gaba ko a dakatar da shi, rahoton Punch.

Gwamna ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kun ji cewa Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya buƙaci ƴan Najeriya su yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu'a.

Oyebanji ya bayyana cewa halin tabarbarewr tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar ɓan ba laifin shugaban ƙasan ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262