'Haduwata Ta Karshe da Ita': Saraki Ya Yi Alhinin Mutuwar Mahaifiyar Yar'adua

'Haduwata Ta Karshe da Ita': Saraki Ya Yi Alhinin Mutuwar Mahaifiyar Yar'adua

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya tuno haduwarsa ta karshe da Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua
  • An ruwaito cewa Hajiya Dada ta rasu tana da shekaru 102 a yammacin ranar Litinin a asibitin koyarwa na Katsina bayan ta yi fama da rashin lafiya
  • Sanata Bukola Saraki wanda ya yi alhinin rasuwar Hajiya Dada, ya yi addu'ar Allah ya sanya mahaifiyar marigayi Yar’adua a Al-Jannah Firdausi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi jimamin rasuwar Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua.

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa mahaifiyar Yar’adua ta rasu tana da shekaru 102 a asibitin koyarwa na Katsina bayan gajeruwar rashin lafiya a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da rasuwar mahaifiyar Yar'Adua, ya fadi alherin da ta shuka

Bukola Saraki ya yi alhinin rasuwar Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua
Bukola Saraki ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Yar'Adua bisa rasuwar Hajiya Dada. Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

"Dada Uwa ce ma bada mama" - Saraki

Saraki ya jajantawa iyalan ‘Yar’adua bisa rasuwar Hajiya Dada, mahaifiya ga marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya tuna haduwarsa ta karshe da marigayiyar inda ya ke cewa ba zai taba mantawa da wannan haduwar ba.

Ya siffanta Hajiya Dada a matsayin uwa ma ba da mama, wadda ke cike da alheri marar iyaka da kuma tausayi.

Haduwar Saraki da Hajiya Dada

A cewar Sanata Saraki:

"Haduwata ta karshe da ita a Katsina haduwa ce da ba zan taba mantawa ba, zan ci gaba da tuna hakan saboda kirkinta da kuma dattako.
"A haduwarmu, na kara yarda da irin girman darajarta da kuma zamanta uwa mai tarin alheri da tausayi. Duk wanda ya santa, zai yi kyakkyawar shaida a kanta.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar tsohon shugaba Yar'adua, Hajiya Dada ta riga mu gidan gaskiya

"A yau, na bi sahun al’ummar kasar domin nuna alhinin rasuwar wannan mata mai dattako. Ina rokon Allah (SWT) ya sanya ta a Aj-Jannah Firdausi."

Tinubu ya yi alhinin Hajiya Dada

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan ‘Yar’adua bisa rasuwar Hajiya Dada.

Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa 'Yar'adua, da marigayi Janar Shehu Musa 'Yar'adua, ta rasu ne a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.