"Ka da Ku Ɗagawa Kowa Ƙafa," Gwamma Abba Ya Kafa Kwamiti kan Abin da Ya Faru a Kano
- Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin da zai gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru lokacin zanga-zanga
- Gwamnan Abba ya buƙaci 'yan kwamitin su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da aka ɗora masu kuma su yi aiki ba sani ba sabo
- Kano na cikin jihohin da zanga-zanga ta yi zafi, bara gurbi sun lalata tare da sace kayayyakin gwamnati da na ƴan kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya kafa kwamitin shari'a wanda zai gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru lokacin zanga-zangar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Kwamitin zai gudanar da bincike mai zurfi kan asarar rayuka, ɓarnatar da dukiyar al'umma wanda aka yi a lokacin zanga-zangar gama gari.
Abba ya ba kwamitin cikakkiyar dama
Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya buƙaci mambobin kwamitin su yi aiki ba sani ba sabo kuma kar su ɗaga wa kowa ƙafa matuƙar suka gano yana da hannu a ɓarnar da aka yi.
Abba Kabir ya faɗawa ƴan kwamitin haka ne a lokacin da yake kaddamar da su a fadar gwamnatinsa da ke birnin Kano.
Gwamna ya ja hankalin ƴan kwamitin
A jawabinsa, Gwamna Abba ya ce:
"Ina amfani da wannan damar wajen sake jaddada cewa mun shirya kuma muna da ƙwarin guiwa za mu iya tunkarar komai kan gaskiyar mu ba tare da la'akari da mai zai je ya dawo ba."
"Saboda haka a madadin gwamnati da ɗaukacin al'ummar jihar Kano muna kira gare ku da ku yi kokarin sauke nauyin da aka ɗora maku cikin gaskiya da jajircewa."
Abba ya bude makarantun da Ganduje ya rufe
A wani rahoton kuma, an ji Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da makarantun kwana 15 na mata waɗanda Abdullahi Ganduje ya soke a zamaninsa.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tuni shirye-shirye suka yi nisa na sake mayar da makarantun na kwana kamar yadda aka sansu a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng