Aisha Abdulkarim: Kotu Ta Rufe Asusu 20 na Wata Mata da Ake Zargi da Ta'addanci a Najeriya

Aisha Abdulkarim: Kotu Ta Rufe Asusu 20 na Wata Mata da Ake Zargi da Ta'addanci a Najeriya

  • Kotu ta ba hukumar DSS uzinin rufe asusu 20 na wata mata da ake zargin tana da alaƙa da ayyukan ta'addanci, Aisha Abdulkarim
  • Mai shari'a Peter Lifu ya umarci DSS ta rike asusun bankunan na tsawon watanni biyu domin gudanar da bincike yadda ya kamata
  • Tun farko lauyan hukumar ƴan sandan farin kayan ya nemi kotun ta amince a rufe asusun na watanni uku domin gudanar da bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba hukumar tsaron farin kaya DSS izinin garƙame asusun banki guda 20 na wata wata mai suna Aisha Abdulkarim.

Kotun ta bada umarnin kulle asusun matar saboda ana zarginta da hannu a ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Mata sun zargi rundunar sojojin kasa, sun nemi a janye dakaru daga yankin Ibo

Jami'an DSS.
Kotu ta umurci DSS ta kulle asusun banki guda 20 da ke da alaka da wata mace ‘yar ta’adda Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

Asusun da ke bankuna takwas, za a ci gaba da rike su har na tsawon kwanaki 60 domin ba hukumar DSS damar gudanar da binciken kwakwaf kan zargin da ake wa matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta bada umarnin rufe asusu 20

Sauran waɗanda ake zargi da ta'addanci tare da Aisha Abdulkarin sun hada da Yehuza Idris da Abdullahi Babayo Umar, duk suna tsare a hannun DSS, rahoton The Cable.

Alkalin kotun, mai shari'a Peter Lifu shi ne ya bayar da umarnin rufe asusun bankunan bayan lauyan DSS, Yunus Umar ya nemi hakan a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1036/2024.

Meyasa DSS ta bukaci karɓe asusun?

Lauyan ya ce yana da muhimmanci a rufe asusun domin baiwa hukumar DSS damar shiga ba tare da wata tangarda ba yayin gudanar da bincike.

Duk da DSS ta nemi a bata izinin rike asusun na watanni uku, alƙalin ya ba hukumar kwanaki 60 kana ya roƙi ta zage dantse wajen kammala binciken.

Kara karanta wannan

Masu zanga zangar da aka kama sun fusata, sun tura zazzafan saƙo ga Tinubu

Vanguard ta ce bankunan da asusun ke ciki sun haɗa da Opay,, Access Bank, UBA, bankin GTB, Union Bank, Moniepoint, First Bank of Nigeria, da kuma bankin FCMB.

Tinubu ya naɗa sabon shugaban DSS

A wani rahoton kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon shugaban hukumar DSS.

Nadin Adeola Ajayi na zuwa ne bayan murabus din Yusuf Magaji Bichi wanda ya ke rike da mukamin tun a shekarar 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262