A Karo Na 2, Ƴan Sanda Sun Gayyaci Shugaban NLC kan Sabon Zargi, Bayanai Sun Fito
- Ƴan sandan Najeriya sun sake gayyatar shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero da sakatarensa, Emma Ugboaja
- Wannan dai na zuwa ne awanni 24 bayan Kwamared Ajaero ya amsa gayyar ƴan sandan a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024
- Rundunar ta buƙaci shugabannin kungiyar kwadagon kasar su hallara a hedkwatarta da ke birnin Abuja ranar 5 ga watan Satumba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kuma gayyatar shugaban kungiyar kwadago ta ƙasa, Joe Ajaero da sakatare, Emma Ugboaja.
Ƴan sandan sun buƙaci shugabannin NLC su kawo kansu hedkwatar rundunar da ke Abuja ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, 2024.
Shugaban NLC ya hallara a ofishin ƴan sanda
Wannan dai na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Kwamared Joe Ajaero ya mutunta gayyatar da ƴan sanda suka yi masa kan zargin hannu a ayyukan ta'addanci, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran dalilan da suka sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci shugaban NLC a farko sun haɗa da zargin aikata laifukan intanet, haɗa baki, da cin amanar ƙasa.
Joe Ajaero ya amsa wannan gayyata kuma ya je hedkwatar ƴan sanda ranar Alhamis da ta gabata, amma bai wuce awa ɗaya ba aka sallame shi bayan ya rubuta bayanai.
Meyasa ƴan sanda suka ƙara gayyatar Ajaero?
A wannan karon, shugaban NLC da babban sakataren ƙungiyar na ƙasa za su amsa tambayoyi daga wurin ƴan sanda kan zargin barazanar aikata miyagun laifuffuka.
Ƴan sanda na ganin barazanar da ake zargin ƴan kwadagon da yi ka iya zama silar ta da zaune tsaye da salwantar da dukiyar gwamnati da ta al'umma.
Sashen tattara bayanan sirri na rundunar ƴan sandan Najeriya ne ya gayyaci shugabannin NLC a ranar 5 ga wata mai kamawa, The Nation ta rahoto.
Me shugaban NLC ya faɗawa ƴan sanda?
A wani rahoton kuma kun ji cewa bayanai sun nuna abubuwan da shugaban kwadago ya tattauna da yan sanda bayan ya amsa gayyatarsu a ranar Alhamis.
An ruwaito cewa zaman ya karkata ne kan wani mai shago da yake zaman haya a sakatariyar yan kwadago a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng