Zargin Ta'addanci: Shugaban NLC Ya Bar Wurin Ƴan Sanda, Ya Koma Hedkwatar Ƴan Kwadago

Zargin Ta'addanci: Shugaban NLC Ya Bar Wurin Ƴan Sanda, Ya Koma Hedkwatar Ƴan Kwadago

  • Shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa, Joe Ajaero ya bar hedkwatar ƴan sanda da ƙarfe 11:15 na safiyar yau Alhamis bayan amsa gayyata
  • Rundunar ƴan sanda ta gayyaci Ajaero ne bisa zarginsa da hannu a ɗaukar nauyin ta'addanci, laifuffukan yanar gizo da cin amanar ƙasa
  • Kwamared Ajaero ya koma hedkwatar NLC da ke Labour House a Abuja amma har yanzun bai yiwa ƴan jarida jawabi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya koma hedkwatar ƙungiyar bayan amsa gayyatar da ‘yan sanda suka yi masa.

Kwamared Ajaero ya isa hedikwatar ƴan sanda da ke Abuja da safiyar ranar Alhamis tare da rakiyar lauya mai kare hakkin dan adam, Femi Falana, SAN, da wasu mutane.

Kara karanta wannan

Daga karshe shugaban NLC ya hallara ofishin 'yan sanda, an samu bayanai

Shugaban NLC da IGP Kayode.
Shugaban NLC ya koma hedkwstar ƙungiyar kwadago bayan amsa gayyatar ƴan sanda Hoto: @NLCheadquaters, @PoliceNG
Asali: Twitter

Shugaban kwadago ya baro hedkwatar NLC

The Nation ta tattaro cewa shugaba kwadagon ya dura hedkwatar ƴan sanda da misalin ƙarfe 10:15 na safe kuma ya bar wurin da ƙarfe 11:15 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Joe Ajaero ya bar wurin ƴan sanda ne bayan ya rubuta bayanansa, kuma bai yi jawabi ga ƴan jarida ba a lokacin da ya fito.

Meyasa ƴan sanda suka gayyaci Ajaero?

Tun farko ‘yan sandan sun gayyaci Ajaero hedikwatar IRT a ranar 20 ga watan Agusta da karfe 10 na safe don amsa tambayoyi kan zarginsa da ɗaukar nauyin ta'addanci.

Har ila yau ƴan sandan suna zargin shugaban NLC da aikata miyagun laifuka ta intanet, haɗa baki, cin amanr ƙasa da yiwa Najeriya zagon ƙasa.

Wannan gayyata da ƴan sanda suka yi wa shugaban kwadagon ya ta da hazo, inda NLC da sauran kungiyoyin kwadago suka fara sukar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya hango illar hana dalibai rubuta WAEC da NECO, ya ba Tinubu shawara

Ƴan kwadago sun zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu da yi wa shugabannin kwadago bita da ƙulli, cewar Channels tv.

TUC ta gano kuskure a farashin fetur

Kuna da labarin kungiyar kwadago ta bayyana kuskuren gwamnatin tarayya da ya jefa al'umma cikin wahala da tsadar man fetur a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ya ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta dauko hanyar shawo kan wahalar man fetur ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262