Gwamnatin Tarayya da ASUU Sun Ɗauki Mataki na Gaba Bayan Ganawa a Abuja

Gwamnatin Tarayya da ASUU Sun Ɗauki Mataki na Gaba Bayan Ganawa a Abuja

  • Gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU sun amince za su sake komawa teburin tattaunawa a watan Satumba
  • Wannan na zuwa ne da ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki daga nan zuwa makonni uku idan gwamnati ta gaza biya mata buƙatu
  • Ministan ilimi na ƙasa, Farfesa Tahir Mamman ya ce za su sake yin zama ranar 6 ga watan Satumba, 2024 da malaman jami'o'in

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Bayan shafe awanni ana tattaunawa, gwamnatin tarayya da ƙungiyar Malaman Jami'o'in sun amince su sake zama a ranar 6 ga watan Satumba, 2024.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan ganawa da shugabannin ASUU yau Laraba, 28 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Matakan da aka ɗauka a taron gwamnatin Tinubu da ASUU sun bayyana

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke.
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun amince za su sake zama a watan Satumba Hoto: ASUU
Asali: Facebook

Kamar yadda Punch ta tattaro, taron ya gudana ne a ma'aikatar ilimi ta tarayya da ke birnin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASUU ta yi barazanar yajin aiki

Idan za ku iya tunawa ASUU ta baiwa gwammatin tarayya wa'adin makonni uku ta biya mata bukatunta ko kuma ta rufe jami'o'in Najeriya.

Malaman jami'o'in sun yi barazanar shiga yajin aiki ne kan dalilai da dama daga ciki har da yarjejeniyar da ASUU ta cimmawa da gwamnati a 2009.

Kazalika na daga cikin bukatun ASUU, gwamnati ta ƙara inganta walwala da jin daɗin malamai, ta ƙara yawan kuɗin tafiyar da jami'o'i da sauransu.

Ministan ilimi zai hana ASUU rufe jami'a

Da yake mayar da martani ga wa'adin da ASUU ta bayar, Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya ce mafi yawan batutuwan da ake ce-ce-ku-ce a kansu sun samo asali ne tun 1981.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar adawa ta dakatar da ɗan Majalisar Tarayya mai ci, ta jero dalilanta

Sai dai ya ce tuni suka aika wasiƙar gayyata ga kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki domin su zo a zauna a lalubo mafita, rahoton Daily Trust.

"Gwamnati ta fara biyan mafi akasarin buƙatun ASUU, alal misali batun cire malaman jami'o'i daga tsarin albashi na IPPIS, tuni shugaban ƙasa ya warware."

Wannan ne ya sa gwamnatin ta zauna da ASUU a Abuja yau, wanda daga karshe aka ɗaga zaman zuwa watan Satumba.

NLC na shirin shiga yajin aiki

A wani rahoton na daban ƙungiyar NLC karkashin Joe Ajaero ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashin wasu daga cikin ma'aikatan jami'a.

Bayan warware takaddamar mafi karancin albashi, kungiyar kwadago ta lashi takobin shiga yajin aikin gama gari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262