'Yan Fansho Sun Tono Tsohon Ƙulli Game da Alƙawarin Tinubu Na Biyan Tallafin N25,000
- Ƴan fansho sun roki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawarin da ya ɗauka na ba ƴan fansho tallafin N25,000
- Mai magana da yawun kungiyar ƴan fansho NUP, Bunmi Ogunkolade ya ce sun yi iya ƙoƙarinsu domin a biya su tallafin rage raɗaɗin amma a banza
- Ya yi ƙara kira ga gwamnatin tarayya ta cika alƙawarin da ta ɗauka wanda tuni ta biya ma'aikata amma ba kyale ƴan fansho
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ƴan fansho sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta cika alƙawarin da ta ɗauka na ƙara masu N25,000 a matsayin tallafin rage raɗaɗin tuge tallafin mai.
Tsofaffin ma'aikatan gwamnatin tarayya sun roki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya waiwaye su bayan ƙarƙare batun mafi karancin albashi.
Yadda Tinubu ya yiwa ƴan fansho alƙawari
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnati ta yi alkawarin cewa za ta biya N35,000 da N25,000 ga ma’aikatan tarayya da ƴan fansho a matsayin tallafin albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin ta ce za ta biya wannan tallafi ne har tsawon watanni shida daga Oktoba 2023 domin rage masu raɗaɗi bayan tuge tallafin man fetur.
Binciken ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta biya tallafin ga ma’aikata, haka wasu jihohi ma sun biya, to amma tsofaffin ma'aikata watau ƴan fansho ba su samu ko ɗaya ba.
Ƴan fansho sun kokawa Bola Tinubu
Da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar ƴan fansho da ke Abuja, mai magana da yawun ƙungiyar NUP Bunmi Ogunkolade, ya nuna rashin jin daɗinsa.
Ya ce sun yi iya bakin koƙarinsu a lokuta da dama domin tunatar da gwamnati ta cika alƙawarin da ta ɗauka na biyansu N25,000 amma babu wani sakamako mai kyau.
A ruwayar Vanguard, Bunmi Ogunkolade ya ce:
"Mun rubuta wasiƙu da dama zuwa ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara, mun kai ziyara a lokuta daban-daban amma ba wani sakamako.
"A ƙarshe sai aka ce mana alƙawarin mu ya maƙale ne saboda matsalar da aka samu a ma'aikatar, haka nan mun kai ƙorafi majalisar tarayya, mun zauna da kwamiti mai kula da ƴan fanssho."
Kakakin kungiyar ƴan fanshon ya ce suna amfani da wannan dama wajen sake kira ga Shugaba Tinubu ya warware batun tallafin rage raɗadin da aka riƙe masu.
Bola Tinubu zai lula ƙasar waje
A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai sake lulawa zuwa ƙasar China domin halartar wasu muhimman tarurruka.
Ziyarar da shugaban ƙasan zai kai zuwa ƙasar China na zuwa ne bayan ya kammala wata ziyara da yaje yi a ƙasar Faransa.
Asali: Legit.ng