Ana Fama da Yunwa, Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ɓarna a Gonakin Mutane a Jihohi 2 na Arewa
- Rahotanni sun nuna ambaliyar ruwa ta yi kaca-kaca da amfanin gonakin al'umma a wasu yankuna da ke jihohin Kebbi da Neja
- Hukumar N-HYPPADEC ta miƙa sakon jaje ga waɗanda ibtila'in ya shafa tare da yabawa matakin gwamnatin tarayya na ware N3bn
- Najeriya na fama da ambaliyar ruwa kusan kowace shekara a jihohi da dama musamman waɗanda ruwa ya gitta ta cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibtila'in ambaliyar ruwa ya lalata amfanin gonakin al'umma a karamar hukumar Argungu da wasu yankunan da dama a jihohin Kebbi da Neja.
Shugaban sashin hulɗa da jama’a na Hukumar bunƙasa wutar lantarki ta ƙasa (N-HYPPADEC), Nura Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Nura Wakil ya miƙa sakon jaje a madadin hukumar zuwa mazauna yankunan da abin da ga shafa musamman manoma, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ambaliya ta jawo koma baya
Hukumar ta ayyana lamarin a matsayin wani gagarumin koma baya ga kokarin da Najeriya ke yi na samar da wadatar abinci mai ɗorewa.
Sanarwar ta ce, Manajan Daraktan Hukumar, Abubakar Yelwa, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ambaliyar ruwan ta shafi rayuwar al’ummar da dama.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa matakin gaggawar da ta dauka na ware ₦3bn domin tallafawa wadanda ibtila'in ya rutsa da su.
Yadda aka riƙa wayar da kan manoma
A baya dai hukumar ta gudanar da gangamin wayar da kan jama’a ta kafafen yada labarai da ziyara wanda hakan ya taimaka wajen rage illar da ambaliyar ruwa ke yi.
Sai dai duk da haka ambaliyar ta ɓarnata amfanin gonaki masu ɗumbin yawamusamman waɗanda ke kusa da ruwa.
N-HYPPADEC ta jaddada bukatar mutane su yi taka tsan-tsan kuma su ɗauki matakan kariya a yankunansu tun kafin faruwar irin haka, rahoton Guardian.
Gwamnatin Kwara za ta ɗauki ma'aikata
A wani rahoton gwamnatin jihar Kwara karkashin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ta ce za ta ɗauki sababbin malaman makaranta da ma'aikata 1,600.
Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya SUBEB, Farfesa Raheem Adaramaja ya ce za a ɗauki ma'aikatan nr domin cike gurbin waɗanda suka yi ritaya.
Asali: Legit.ng