Gwamna a Arewa Zai Rage Yawan Masu Zaman Kashe Wando, Zai Ɗauki Ma'aikata

Gwamna a Arewa Zai Rage Yawan Masu Zaman Kashe Wando, Zai Ɗauki Ma'aikata

  • Gwamnatin jihar Kwara karkashin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ta ce za ta ɗauki sababbin malaman makaranta da ma'aikata 1,600
  • Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya SUBEB, Farfesa Raheem Adaramaja ya ce za a ɗauki ma'aikatan nr domin cike gurbin waɗanda suka yi ritaya
  • Ya ce za a bi tsarin da ya fi kusa da al'umma wajen ɗaukar ma'aikatan kuma sai wanda ya cancanta za a ɗauka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kwara ta shirya daukar jimillar ma’aikatan da malaman makaranta 1,600 daga fadin kananan hukumomi 16 na jihar.

Shugaban hukumar Farfesa Raheem Adaramaja ne ya bayyana hakan ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.
Gwamnan Kwara zai ɗauki ma'aikata da malaman makaranta Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Twitter

Gwamna ya bada izinin ɗaukar malamai

A wata sanarwa da sakatariyar yada labaran hukumar, Atere Ameenat ta fitar, ta ce za a ɗauki ma'aikatan ne bisa umarnin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ameenat ta bayyana cewa Gwamna Abdulrazaq ne ya ba da umarnin ɗaukar malamai da ma'aikatan domin cike gurbin da ake da shi, Punch ta rahoto.

Dangane da tsarin da za a bi wajen daukar ma’aikatan, sanarwar ta jaddada cewa za a yi amfani da tsarin mafi kusa da al’umma ba tare da tauye kwarewa da cancanta ba.

Tsarin da za a ɗauki ma'aikata a Kwara

Sanarwar ta ce:

"Za a ɗauki ma'aikatan da malaman a matakin ƙananan hukumomi ko a garuruwan da suka fi buƙatarsu, waɗanda aka ɗauka za su sa hannu a yarjejeniyar ba za su canza wurin zama ba na shekara biyar."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fara baje kolin ayyukansu a TikTok, an hango illar hakan ga tsaro

Shugaban hukumar iliminz Farfesa Raheem ya ce hakan ya yi daidai da kudurin gwamnan na inganta fannin ilimi, musamman a matakin kananan hukumomi.

A cewar shugaban SUBEB ta jihar Kwara, za a ɗauki mako uku ana aikin tantance masu neman aikin daga ranar da aka fara.

Majalisa fa aika saƙo ga Gwamnan Kano

A wani rahoton kuma majalisar dokokin Kano ta nemi gwamnatin jihar ta dauki matakan taimako na gaggawa kan ambaliyar ruwa.

Ɗan majalisa da ke wakiltar Gabasawa, Zakariya Abdullahi ya ce ambaliya ta yi mummunar ta'adi a yankinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262