Ambaliya: An Gano Adadin Wadanda Su ka Mutu da Rasa Muhallansu a Jihohin Arewa 3

Ambaliya: An Gano Adadin Wadanda Su ka Mutu da Rasa Muhallansu a Jihohin Arewa 3

  • Iftila'in ambaliyar ruwa na cigaba da muguwar ɓarnar rayuka a jihohin Arewacin kasar nan
  • An lissafa gidaje akalla sama da 41,000 da ambaliya ya lalata, musamman a Arewa maso Gabas
  • A jihohi uku kawai da hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta fitar, akalla mutum 41 sun mutu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya kashe akalla mutane 49 a Arewa maso Gabas.

Haka kuma an samu jihar Arewa maso Yamma ɗaya - Jigawa, da ta fuskanci matsanancin ambaliya a damunar ba.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

Ambaliya
Akalla mutane 29 sun rasu sakamakon ambaliya Hoto: Dan Alheri/Mustapha Moh'd Gujba banker
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce aƙalla mutane 41,344 sun rasa muhallansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin da iftila'in ya fi shafa a wannan lissafin sun hada da Taraba da Adamawa da ke Arewa maso Gabas, sai Jigawa da ke Arewa maso Yamma.

"Yanzu aka fara ambaliya," NEMA

Jami'in hulda da jama'a na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta bayyana cewa yanzu aka fara shiga lokacin ambaliya, musamman a Arewa.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Manzo Ezekiel a shekarar 2023 ne aka samu ambaliya mafi muni a kasar nan.

Channels Television ta wallafa cewa akalla mutane 600 ne su ka mutu, yayin da wasu miliyan 1.4 million su ka rasa gidajensu, an rasa gonaki 440,000 a 2023.

"An tafka asarar saboda ambaliya," Jigawa SEMA

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

Hukumar bayar da agaji a Jigawa (SEMA) ta ce an rasa kadada 11,560 na gonaki a Jigawa.

Shugaban hukumar SEMA a Jigawa, Dr. Haruna Mairiga ya shaidawa Legit cewa an kuma rasa gidaje akalla 7,060.

Dr. Mairiga ya bayyana fargaba kan karuwar ambaliya ganin cewa har yanzu ana cikin mamakon ruwan sama.

Ambaliya ta rusa sama da gidaje 100

A baya mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar rushewar gidaje akalla guda 100 a jihar Jigawa, inda mutane su ka fara neman mafaka.

Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta bayyana cewa su na agazawa wadanda lamarin ya shafa, sannan ana tsare kayansu saboda kar ɓata-gari su yi masu sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.