"Ba Mu da Labari," Ƴan Sanda Sun Yi Magana Kan Sace Mutane 150 Bayan Kisan Sarkin Gobir

"Ba Mu da Labari," Ƴan Sanda Sun Yi Magana Kan Sace Mutane 150 Bayan Kisan Sarkin Gobir

  • Ƴan sanda sun sanar da cewa ba su samu rahoto a hukumamce kan labarin sace akalla mutane 150 a yankin Sabon Birni a jihar Sakkato ba
  • Mai magana da yawun ƴan sandan Sakkwato, ASP Ahmed Rufai ya ce abin da aka kawo masu rahoto ne kaɗai za a ji daga bakinsu
  • Duk da ya amince akwai barazanar tsaro a Sabon Birni, kakakin ƴan sandan ya ce mutane ba su iya kawo masu rahoto saboda tsoro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta musanta labarin sace mutane sama da 150 a Sabon Birni kwanaki kadan bayan kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir.

A wata hira da RFI Hausa ranar Asabar da ta wuce, Farfesa Bello Bada na jami'ar Usman Ɗan-Fodio ya yi ikirarin cewa an sace akalla mutane 150.

Kara karanta wannan

"Ba Allah ya kawo mana talauci ba," Tsohon shugaban ƙasa ya ja kunnen shugabanni

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Rundunar ƴan sanda ba ta da masaniyar sace mutane sama da 150 a Sakkwato Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Ya bindiga sun ɗauki mutane a Gobir

Ya ce ƴan fashin dajin sun yi garkuwa da waɗannan mutane ne tsakanin lokacin da aka kashe sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa zuwa ranar Jumua, Channels ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya kuma taɓo abubuwan da yake zargin sune suka jawo matsalar ƴan bindiga da garkuwa da mutane a Arewacin Najeriya..

Malamin jami'ar ya ce ba wannan ne karon farko da ake kai wa manyan mutane hari ba, amma shi ne na farko da aka yi wa wani sarki mummunan kisan gilla.

Ƴan sanda ba su da masaniya

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce ‘yan sandan ba su da masaniyar sace mutanen.

Ƴa ce rundunar ƴan sanda tana tabbatar da hare-hare da duk abin da aka kawo mata rahoto a hukumance amma wanda ba ta sani ba, ba za ta iya cewa uffan ba a kai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi awon gaba da babban jami'in gwammati a Najeriya

Amma kakakin ƴan sandan ya ce babu tantama yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni da shiyyar Sakkwato ta Gabas gaba ɗaya suna fuskantar barazanar tsaro.

ASP Ahmed Rufai ya ce galibin mazauna yankin na jin tsoron su gayawa jami'an tsaro abubuwan da ke faruwa saboda abin da ka iya zuwa ya dawo.

Matasa za su maka gwamna a kotu

A wani rahoton kun ji cewa ƙungiyoyin matasa a Sokoto sun dauki haramar maka gwamnati a kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya kan kisan Sarkin Gobir.

Jagoran matasan, Sulaiman Shuaibu Shinkafi ya bayyana sharudan da suka ba gwamnatin ta cika a kan lokaci ko kuma su hadu a kotun ICC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262