'Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Yi Awon Gaba da Babban Jami'in Gwammati a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Yi Awon Gaba da Babban Jami'in Gwammati a Najeriya

  • Ƴan bindiga sun sace wani darakta da ke aiki a hukumar tattara kuɗaden shiga ta jihar Ribas, Sir Aribibia John Fubara
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta a iska kafin daga bisani su tasa abin harin su zuwa wurin da har yanzun ba a gano ba
  • Rundunar ƴan sandan jihar Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami'an tsaro sun bazama domin farauto maharan duk inda suka shiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani darakta da ke aiki a hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Rivers a Fatakwal.

‘Yan bindigar wanda ba su wuce su shida ba a kan wani jirgin ruwa mai gudu, sun sace daraktan a tashar jiragen ruwa da ke babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

IGP Kayode da tawagarsa.
Yan bindiga sun sace daraktan hukumar tara kuɗin shiga a jihar Rivers Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta tattaro, maharan sun yi awon gaba da babban jami'in gwamnatin zuwa wani wuri da ba a sani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigar sun buɗe wuta

An tattaro cewa maharan sun yi ɓarin wuta a iska don tsorata mutane gabannin su ɗauko abin harinsu wanda aka bayyana sunansa da Sir Aribibia John Fubara.

Ƙaramin ƙanin wanda ƴan bindigar suka yi garkuwa da shi mai suna, Emmanuel Fubara ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya bayyana cewa tuni aka gaggauta sanar da ƴan sanda abin da ya faru domin ɗaukar matakan kubutar da shi.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Bugu da ƙari, jami'ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan (PPRO) SP Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Punch ta rahoto.

"Rundunar ƴan sanda ta samu labari kuma tuni kwamishina ya umarci dakarun ƴan sanda na sashin dabaru su tabbatar sun ceto mutumin cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gaji da halin 'yan kwangila, ana shirin daukar mataki kan masu algus

"Yanzu haka jami'an ƴan sanda sun fara farautar maharan domin ceto dataktan da aka sace, da cafke maharan su gurbi abin da suka shuka a gaban ƙuliya," in ji SP Grace.

An kashe ɗan basarake a Legas

A wani rahoton kuma an shiga jimami a jihar Legas bayan ƴan bindiga sun hallaka yaron wani basarake mai sarautar Ojomu na Ajiran.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka shi ne a ranar Litinin, 26 ga watan Agustan 2024 a yankin Agungi da ke Lekki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262