Ambaliyar Ruwa: Ministan Tsaro Ya Ba da Tallafi Ga Mutanen Jihar Jigawa

Ambaliyar Ruwa: Ministan Tsaro Ya Ba da Tallafi Ga Mutanen Jihar Jigawa

  • Minista tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru ya tuna da al'ummar da annobar ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar Jigawa
  • Badaru ya ba da tallafin N20m ga gwamnatin jihar domin taimaka mata a ƙoƙarin da take yi na tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta ritsa da su
  • Ministan tsaron ya ba da tallafin ne lokacin da yaje yin jaje ga gwamnan jihar Umar Namadi kan ambaliyar ruwan wacce ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Ministan tsaro Mohammed Badaru ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.

Ministan ya ba da tallafin N20m ga gwamnatin jihar Jigawa a ƙoƙarin da take na tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.

Kara karanta wannan

Wike ya yi maganar yiwuwar sasantawa kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Badaru ya ba da tallafi a Jigawa
Badaru ya ba da tallafin N20m saboda ambaliyar ruwa a Jigawa Hoto: Buhari Hussaini
Asali: Facebook

Badaru ya ba da tallafin N20m

Mohammed Badaru ya ba da tallafin ne lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Jigawa domin yi masa jaje kan ambaliyar ruwan wacce ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar tsaro, Mista Henshaw Ogubike, ya fitar ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

A cewar Henry Ogbuike, ministan tsaron ya nuna tausayinsa kan ambaliyar ruwan wacce ta yi sanadiyyar lalata gonaki masu yawa a jihar..

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya a shirye take domin tallafawa jihar, yayinn da ya yi bayanin cewa tallafin na sa na ƙashin ƙansa domin taimakawa jihar bisa wannan mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki.

Badaru ya kuma yabawa gwamnan jihar, Umar Namadi kan yadda ya ɗauki matakan kai agaji cikin gaggawa sakamakon ambaliyar ruwan.

Kara karanta wannan

Jigawa: Mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwa sun kai 28, gwamna ya jero dalilai

Badaru ya yabawa Gwamna Namadi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, ya ce ayyukan ci gaban da Gwamna Umar Namadi ya kinkimo ya ƙara wanke shi daga nuna shi a matsayin magajinsa.

Badaru, wanda yanzu shi ne ministan tsaron Najeriya, ya ziyarci Jigawa inda ya aza harsashin gina gidaje masu tarin yawa na jihar a Panisau, wani yanki da ke bayan garin Dutse, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng