Ana Gayyatar Mutane Tarban Sanusi II daga Landan Yayin da Aminu Ado Ya Bar Kano

Ana Gayyatar Mutane Tarban Sanusi II daga Landan Yayin da Aminu Ado Ya Bar Kano

  • Muhammadu Sanusi II ya yi nasarar kammala karatunsa na digiri na uku watau PhD a jami’ar SOAS a Ingila
  • Hajiya Sa’adatu Baba Ahmad ta fitar da sanarwa cewa jama’a su fito su tarbi Sarkin Kano a safiyar ranar Lahadi
  • Mai martaba Sarkin Kano zai dawo daga Birtaniya, tawagarsa za ta yi yawo a cikin gari kafin ya shiga fada

Kano - A halin yanzu mutane suna ta taya Muhammadu Sanusi II murnar kammala digirinsa na PhD a jami’ar SOAS a Landan.

Bayan ya kammala aikinsa kuma ya gabatar da binciken da ya yi, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai dawo gida a gobe.

Sarkin Kano
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zai dawo daga Landan Hoto: Ibrahim Sanyi Sanyi
Asali: Facebook

Muhammadu Sanusi II zai dawo Kano

Sa’adatu Baba Ahmad ta fitar da sanarwa a shafinta na Facebook cewa ana sa ran Mai martaba zai dawo gida a safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sanusi II, Obasanjo, Gowon da wasu shugabannin da suka koma aji neman PhD

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ta shelantawa masoya Sarkin Kano, Sa’adatu Baba Ahmad ta ce Sanusi II zai iso da kimanin karfe 9:30 na safiyar ranar.

Idan Mai martaba ya baro tashar sauka da tashin jirgin sama na Kano, zai wuce fadarsa.

Sanusi II zai dawo, Aminu Ado ya tafi

A lokacin da zai iso, babu mamaki shi kuma Aminu Ado Bayero ya na Abuja inda aka bayyana cewa Sarki na 15 zai halarci wani taro.

Kafin yanzu Mai martaba Aminu Ado Bayero ya tare a Kano duk da gwamnati ta tsige shi a sakamakon rusa sababbin sarakunan jihar.

Sarkin Kano Sanusi II zai zagaye gari

Tawagar Khalifa Muhammadu Sanusi II za ta bi ta titin Ibrahim Badamasi Babangida zuwa masallacin idi har ya isa Kofar Mota a Kano.

Sanarwar ta ce daga Kofar mata, Mai martaba Khalifa Sanusi II zai ratsa ta masallacin cikin gari, sai ya shiga fada ta Kofar Kudu.

Kara karanta wannan

A karon farko bayan fara rikicin sarauta, Sarki na 15 Aminu Ado ya fita daga Kano

Sanarwar tarbar Muhammadu Sanusi II

“Ana gayyatar Jama’a zuwa taren Mai Martaba Sarkin Kano, Khaleefa Dr. Muhammad Sanusi II, wanda zai dawo daga tafiyar da ya yi ƙasar waje ranar Lahadi 25th August, 2024 da misalin karfa 9:30am na safe."

"Mai Martaba zai taho daga airport zuwa gidansa na cikin birni ta Titin IBB zuwa Masallacin Idi zuwa ƙofar Mata zuwa Masallacin cikin Gari sannan ya shiga gidan sa ta ƙofar Kudu. Muna adduar Allah ya kawo Sarki lafiya ya samemu lafiya.”

- Sa'adatu Baba Ahmad

Shugabannin da Sanusi II ya bi sahunsu

Kafin Muhammadu Sanusi II ya koma aji, kun ji labari Olusegun Obasanjo da Yakubu Gowon sun samu PhD ne bayan barin mulki.

A lokacin Nasir El-Rufai yana gwamna ya tafi karatu a wata jami’ar Netherlands, hakan ta faru da Rabiu Kwankwaso a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng